Gwamna Matawalle Ya Gayyaci Duk Almajiran Da Aka Fatattaka A Jahohin Arewa

0
615

Daga Wakilanmu

GWAMNAN jahar Zamfara, Bello Matawalle na maraba da duk almajiran da aka fatattaka daga jahohin Arewa su koma jaharsa, sa’annan ya dakatar da batun hana almajiranci gaba daya.

Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Yusuf Idris cikin wata sanarwa da ya fitar, inda yace gwamnatinsa ba zata kori almajirai ba.

Tun bayan barkewar cutar Coronavirus ne gwamnoni suka fara fatattakar almajirai daga jahohinsu, a wani mataki na kare su daga cutar, da kawo karshen tsarin almajiranci gaba daya.

A yanzu haka Gwamnonin jahohin Arewacin Najeriya na nazari game da tsarin da ya kamata su dabbaka wajen kawo karshen almajiranci a yankin.

Sai dai a jawabinsa, Gwamna Matawalle ya ce “Gwamnati ba za ta kori almajirai zuwa jahohinsu na asali ba, duk wadanda aka kora daga sauran jahohi ma muna maraba da su, su dawo Zamfara, za mu kula da su.”

Matawalle ya sauya ra’ayinsa ne bayan wata ganawa da ya yi da manyan malamai guda 3; Abdullahi Dallah-Dallah, limamin Masallacin Dan Ashafa da kuma Sheikh Bello Kanwa.

Jim kadan bayan ganawa da wadannan Malamai ne sai Gwamnan ya sanar da soke kwamitin da ya kafa na hana almajiranci a jahar.

“Mun yanke shawarar ne bayan nazarin almajiranci a jahar, tare da bukatar hada shi da tsarin karatun zamani na boko don samar wa almajirai ingantaccen ilimin zamani da na addini.

“Mun fasa fatattakar almajiran ne don nuna musu ana tare, su ma mutane ne, tare da rage kyamar da ake nuna wa karatun almajiranci a kasar nan. Almajirai na da damar samun ingantaccen ilimi a kowanne mataki a kasar.” Inji shi.

Daga karshe gwamnan yace a yanzu ya dukufa don samar da sahihin tsari da zai hada karatun almajirci da na boko a jahar ta yadda zai amfani almajiran, ba wai sallamar su daga jahar ba.

Su ma a nasu jawabin, Sheikh Dallah-Dallah da Sheikh Kanwa sun jinjina wa Gwamnan bisa matakin da ya dauka, kuma sun yi kira a gare shi ya gudanar da mulki na adalci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here