Jami’an DSS Sun Kama Mutumin Da Ya Yi Garkuwa Da Jikan Dahiru Bauchi

0
412

Daga Usman Nasidi.

JAMI’AN hukumar tsaro ta sirri, DSS, ta sanar da kama mutumin da ya yi garkuwa da jikan fitaccen Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi, mai shekaru 3 a duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa baya ga kama mutumin, jami’an na DSS sun kubutar da yaron cikin ruwan sanyi tare da kwato kudaden fansar da iyayensa suka biya don a sake shi.

A ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu aka yi garkuwa da yaron a gidan Shehin da ke jahar Kano. Shugaban hukumar DSS reshen jahar Kano, Muhammad Alhassan ya tabbatar da lamarin.

Muhammad Alhassan ya bayyana cewa sun samu nasarar kama mutumin ne tare da hadin gwiwar hukumar ‘yan sandan jahar Kano.

“Mun samu nasarar cafko wanda ake zargi da aikata laifin ne ta hanyar hadin gwiwa wajen musayar bayanan sirri a Kano. Da fari mutumin dan shekara 27 mai suna Umar Ahmad ya nemi a ba shi Naira Miliyan 10 kudin fansa.

“Daga bisani ya rage zuwa miliyan 6, nan da nan muka shiga bin sawunsa har muka gano mabuyarsa a daki na 27 na Hotel din Liberty a cikin titin Aba Road na unguwar Sabon Gari, jahar Kano.

“Bayan mun far ma otal din, sai muka kubutar da yaron, wanda a yanzu haka yana cikin koshin lafiya, muka kama mutumin da ya yi garkuwa da shi, sa’annan muka kwato kudaden da aka biya shi, ta hanyar kwashe su daga asusun bankinsa.” Inji shi.

Daga karshe Alhassan ya ce za su mika mutumin ga ‘yan sanda don su gurfanar da shi gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here