Buhari Na Kiran A Yi Noma Ne Domin Ya Taimaki Kasa Da Tattalin Arzikinta – Tijjani Bambale

0
405

Mustapha Imrana Abdullahi

WANI mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum Alhaji Tijjani Bambale, ya bayyana kiraye-kirayen da shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari ke yi wa manoma na su tashi tsaye domin samar da abinci a kasa da cewa abu ne wanda ya dace kuma ya nuna irin yadda shugaba Buhari ke kishin kasar da al’ummarta baki daya.

Alhaji Tijjani Bambale ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawar da ya yi da wakilinmu ta manhajar whatsapp, saboda wannan hanya da shugaban kasa ke magana a kanta a tashi a yi Noma ita ce mai bullewa a gare mu, domin an gina Nijeriya ne tun asali ta hanayar Noma. Ganin an gina Nijeriya da duk wani tattalin arzikin da muke takama da shi tun asali ta hanyar Noma ya zama wajibi mu ci gaba da rike shi. Saboda shi ne mafi alfanu gare mu ko a nan gaba.

Tun fa ba mu zama komai ba har a yanzu muka zama komai, kuma makomar tattalin arzikin duniya da a gare mu shi ne mu rike Noman nan shi me mafita gare mu, ta yadda ko da an shiga cikin wani hali na tabarbarewar tattalin arziki a duniya mu ba za mu tagayyara ba saboda a kullum kayan abinci sai an neme su a kowane hali aka shiga.

Mutane su duba yanayin da aka shiga a bangaren tattalin arzikin mai , amma idan batun Noma ne wane ne zai ce batun abinci ya shiga hali a duk duniya dole ne a nemi abinci a kowane hali aka shiga domin mutum bai yi sai da abinci.

Kuma shi shugaban kasa na kiraye-kirayen a yi Noma ne domin ya taimaki kasar da tattalin arzikinta baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here