An Sace Shugaban Kungiyar Kiristoci Ta Kasa Reshen Nasarawa

0
399

Mustapha Imrana Abdullahi

TSOHON sakataren kungiyar CAN  Yohanna Samari, ya tabbatar wa da kafar yada labarai ta Resiyon gwamnatin tarayya ( FRCN) cewa wadansu da ba a san ko su wane ne ba sun sace shugaban kungiyar Kiristoci reshen Jihar Nasarawa Bishop Joseph Masin da sula shigo cikin gidansa a Bukan Sidi a garin lafiya Jihar Nasarwa.

Yohanna Samari ya ce mutanen sun zo ne da misalin karfe 11 na daren ranar Laraba zuwa karfe 12 na talatainin dare.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Mista Bola Longe ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya kara da cewa wadanda suka sace shugaban kungiyar kiristocin sun dauke shi ne a kan Baburan hawa.

Bola Longe ya kuma tabbatar wa da manema labarai cewa jami’an ‘yan sanda na iya bakin kokarinsu domin tabbatar da kubutar da shugaban kungiyar na CAN.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here