Shugaba Buhari Ya Jajanta Wa Mutanen Sakkwato

0
315

Rahoton Z A Sada

SHUGABAN kasa, Muhammadu Buhari ya janjanta wa iyalan waɗanda suka rasa ransu a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaban ya yi addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka samu raunuka.

Shugaban ya bayyana cewa abin takaici ne a ce ‘yan bindiga suna kai hare-hare a irin wannan lokaci da duniya da Najeriya ke fama da annobar korona.

Shugaban ya yi alkawarin cewa rundunar da aka ƙaddamar domin yaƙar masu tayar da ƙayar baya a arewa maso yammacin ƙasar za ta ci gaba da yaƙar ‘yan bindigar da suka addabi yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here