A Yi Koyi Da Masallacin Sultan Bello Kaduna – Na Barazil

0
310
An yi kira ga Gwamnati da kuma sauran daukacin al’ummar musulmi duniya baki daya da su yi koyi da masallacin Sultan Bello da ke cikin garin Kaduna.
Kiran ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar masu sayar da motoci reshen Jihar Kaduna Alhaji Ahmad Nabirazil ne ya yi wannan kiran lokacin da yake zantawa da manema labarai a kaduna.
“Bari in yi tsokaci a kan yadda na ga an yi Sallah a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, misali idan aka yi sahu na farko tsakanin mutum da mutum akwai tazara, sai kuma sahun baya babu kowa sai a yi sahu a layi na uku shi ma kuma akwai tazara tsakanin mutum da mutum kuma shi ma sahun baya na kusa da shi ba kowa, haka dai aka yi domin kiyaye lafiyar jama’a”.
Na Brazil, ya kuma yi kira ga Gwamnati da ta sassauta a game da batun yi wa mutane tara a kan rashin sanya takunkumi a Kaduna domin wadansu ba su da kudin da za su iya sayen takunkumin sakamakon irin halin da jama’a suke ciki sanadiyyar cutar Covid – 19 da ake kira da Korona bairus.
Ya ci gaba da cewa hakika Gwamnati na yin wadansu abubuwa ne domin ciyar da kasa da al’ummarta gaba tare da batun kare lafiyar jama’a, amma a wannan lokaci ana cikin wani mawuyacin hali, don haka sai an sassauta wa jama’a, saboda haka muke kiran Gwamnati lallai ta duba yanayin da ake ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here