An Sako Limamin Da Ya Ja Sallar Juma’a A Zariya

0
369

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

AN sako Limamin da jami’an tsaro suka kama a kan jan sallar Juma’a a garin Zariya bayan kwanaki hudu da ya kwashe a wurin ‘yan sanda .

A yayin da aka tuntubi limamin a jiya Juma’a, Malam Muhammad Tukur ya ki yin tsokaci don ya ce Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa iqamatis Sunnah ta Zariya ta umarcesa da ya yi shiru.

Amma kuma, ya tabbatar da cewa an sako shi a ranar Laraba bayan an kai shi gaban kotu .

Bayan kama Idris da aka yi a ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, Malam Sani Yakubu, shugaban kungiyar JIBWIS reshen Zaria ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Daya daga cikin mamun ya tabbatar da cewa sun yi sallar Juma’a din ne saboda watan Ramadana mai alfarma ne.

Ya kara da cewa: “Saboda ba mu yi sallar Juma’a ba na makonni tara, mun bukaci Malam Tukur da ya ja mu sallar Juma’a akalla ko ta karshe ce a watan Ramadana. Gaskiya ba shi ya shirya sallar ba.

“An rokesa ne kuma ya amince. Mu mutane ne masu son zaman lafiya don haka ne ya sa muke biye da dokokin gwamnati. Amma ba za mu zuba ido ana wulakanta malamanmu ba.”

Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta zirga-zirga tare da hana dukkan wuraren bauta budewa don dakile yaduwar annobar Coronavirus a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here