2023: Cin Zaben APC Akwai Mushkila – Injiniya Kailani

  0
  359
  Mustapha Imrana Abdullahi
  WANI jigo a jam’iyyar APC Injiniya Dakta Kailani Muhammad ya bayyana cewa in ba a yi gyara ba cin zaben jam’iyyar APC a shekarar 2023 akwai mushkila.
  Injiniya Kailani Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
  Inda ya ce hakika idan ana son APC ta ci zabe a shekarar 2023 dole sai an yi gyara in ba haka ba lamarin cin zabe ba zai yiwu ba.
  A matsayina na dan jam’iyyar APC ya dace kowa ya sani cewa akwai gyara kuma dole ne a aiwatar da shi.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here