Mutane 12 Sun Yi Fiye Da Wata 2 Suna Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyade A Jigawa

0
531

Rahoton Z A Sada

WATA yarinya mai shekara 12 ta shaida wa ‘yan sanda a Jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya cewa wasu mutum 12 sun shafe wata biyu suna yi mata fyade.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta shaida wa BBC cewa ta samu ƙorafin cewa wani mutum mai shekara 57 ya yi ta yaudarar yarinyar a wani keɓantaccen waje don ya yi lalata da ita.

A yayin wata hira da ‘yan sanda, yarinyar ta ce baya ga wannan mutumin wasu mazan 11 sun shafe wata biyu suna yi mata fyade. Tuni rundunar ‘yan sandan ta kama wasu mutum 12 da ake zargi.

Wani mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ya faɗa wa BBC cewa an kai yarinyar asibiti kuma binciken likitoci ya tabbatar da cewa an yi mata fyade. Amma ana ci gaba da bincike.

Lamarin na zuwa ne a yayin da aka kashe wasu mata biyu a wurare daban-daban a Najeriya, al’amarin da ya jawo tashin hankali. A makon da ya gabata aka kashe wata daliba ‘yar shekara 22. An kashe Uwavera Omozuwa da abin kashe gobara wato fire extinguisher.

A ranar Laraba ne ɗalibar mai shekara 22 da ke nazarin ilimin ƙananan halittu ta je cocin Redeemed da ke kusa da jami’ar domin yin karatu, kamar yadda ta saba, inda aka je aka same ta yashe a ƙasa jina-jina.

A wannan makon ne dai kuma aka yi wani rikicin sakamaon harbe wata matashiya ‘yar shekara 16 mai suna Tina Ezekwe da ‘yan sanda suka yi a Legas. Hukumomi sun ce an kama jami’an biyu da ke da alaka da kisan.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce duk da cewa fyade laifi ne babba a Najeriya, ana samun ƙaruwar aikata shi ne saboda rashin hukunta masu yi a ƙasar. Ba a fiya yi wa masu fyade hukunci ba a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here