Rahoton Z A Sada
TSOHON Gwamnan jihar Imo kuma Sanata a yanzu Rochas Okorocha, ya soki gwamnonin arewa kan hana almajirci.
Sanatan ya nemi a inganta almajirci inda ya yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su taimaka wa tsarin.
Rochas ya ce “mafi yawancin manyan da ke gare mu a yanzu sun yi almajirci.”
Okorocha ya ce gidauniyarsa na da makarantu a Kano da Zariya da Yola da Sakkwato, kuma duka almajirai yake taimaka wa domin su samu ilimi.
An daɗe ana ce-ce-ku-ce kan batun almajirci a Najeriya musamman illolinsa da kuma makomar yaran da ake tura wa almajiranci.