Akwai Rufin Asiri A Kasuwancin Sayar Da Katako-Malam Sulaiman

  0
  488
  Malam Sulaiman Mu’azu Sarki

  Isah Ahmed Daga  Jos

  MALAM Sulaiman Mu’azu Sarki, wani dattijo ne da ya kwashe sama da shekaru 40, ya harkar kasuwancin sayar da Katako,  a  kasuwar ‘yan katako da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato.

  A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana yadda ya fara wannan kasuwanci na sayar da Katako, da kuma yadda kasuwancin yake. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK: A wannan lokaci ne ka fara wannan kasuwanci na sayar da katako?

  Malam Sulaiman: To da farko dai na fara da sanar kafinta ne. Shi ne daga baya, na sami cigaba na barwa yara wannan sana’a,  na kama kasuwancin sayar da katako a wannan kasuwar katako ta Jos. Kuma na fara wannan kasuwanci ne, tun a shekara ta 1978, wato shekaru 42 da suka gabata.

  Wannan kasuwar Katako da ke garin Jos Iyamurai ne suka fara zuwa, tun a shekara ta 1975. Daga nan sai hausawa suka zo, ina daya daga cikin hausawan da suka fara zuwa wannan kasuwa.

  A yanzu ina da shekaru 65 da haihuwa, kuma ina da yara 22. 

  GTK: Yaya za ka bayyana mana mahimmancin wannan kasuwanci, na sayar da katako?

  Malam Sulaiman: Gaskiya harkokin kasuwanci katako abu ne mai matukar mahimmanci. Domin duk wanda Allah ya ba shi ikon yin wannan kasuwanci, kuma ya tafiyar da shi bisa adalci zai sami ci gaba sosai. Domin idan mutum yana kasuwancin sayar da katako zai iya rike yara kamar 10 wadanda zasu rika taya shi wannan kasuwanci.

  Babu shakka  akwai rufin asiri a wannan kasuwanci.  Idan har mutum bai tsawalla rayuwa ba, in Allah ya yarda zai sami rufin asiri.

  Badan Allah ya kawo mu wannan hali na annobar Kurona da muke ciki ba. Kamar a  wannan lokaci  na watan hudu zuwa watan biyar, gaskiya kasuwancin katako yana tafiya kwarai da gaske. Domin a irin wannan lokaci mutane masu ginin kasa, suna zuwa sayen katako, don haka a irin wannan lokaci kasuwancin yana tafiya sosai.

  Kuma wannan kasuwanci yana da daukar dawainiyar gida, ka ga wannan shi ne babban rufin asiri. Idan ka shigo da jari kadan, idan Allah ya yarda cikin lokaci kankani, sai ka ga ka yi sama matukar ka rike gaskiya.

  Kuma wannan kasuwanci na sayar da katako, kasuwanci ne na yau da kullum, domin babu yadda za a yi a daina yinsa. Kullum duniya ci gaba ake yi, kuma duk ci gaban da duniya take yi, dole sai an hada da katako. Don haka muna yi wa Allah godiya da wannan kasuwanci.

  GTK: Wadanne irin nasarori ne ka samu a wannan kasuwanci,  daga lokacin da kafa fara zuwa yanzu?

  Malam Sulaiman: Gaskiya na sami nasarori da dama, domin nayi muhalli kuma ina biyawa yarana kudin makaranta. Kuma na yaye yara da dama a wannan kasuwanci, wadanda sun koya kuma sun je sun bude nasu wararen kasuwancin.

  GTK: Wadanne irin matsaloli ne kuke fuskanta a wannan kasuwanci?

  Malam Sulaiman: Matsalolin kasuwancin sayar da Katako da muke fuskanta ta farko, ita ne  matsalar sufuri.  Wato yadda ake dauko Katako daga daji, a kawo cikin gari. Saboda ba kowace mota ce take zuwa ta dauko Katako daga daji ta kawo cikin gari ba.

  Sannan kuma wani lokaci akwai matsalar kai mai sayen Katako, kana zaune a cikin gari sai bayar da kudi a daji, don a yanko maka Katako, sai a dauki lokaci, ba ka samu ba.

  GTK: Kamar ya ya farashin katako yake a yanzu?

  Malam Sulaiman: Farashin katako yana dadewa bai tashi ba, kamar sauran kayayyaki. Domin farashin Katako a wannan kasuwa, kamar shekaru uku da suka gabata, bai canza ba.

   Kuma kamar a nan Filato, mun fi wurare da dama saukin  farashin Katako, domin akwai banbanci da sauran wurare. Saboda  mu muna da wuraren samun katakon, fiye da sauran wurare, kuma bamu da yawan al’umma, don haka katako yake da sauki, a wannan kasuwa.

  GTK: Kamar daga wadanne wurare ne kuke sayo wannan Katako, kuma daga wadanne wurare ne kuke samun wadanda suke zuwa  su saya?

  Malam Sulaiman: Muna samun wannan Katako kamar daga yankunan  jihohin Kaduna da Filato da Bauchi.  Kuma muna samun masu zuwa saye  daga Kaduna da Bauchi da Nasarawa da kuma nan garin Jos.

  GTK: Wanne kira ne kake da shi zuwa ga masu wannan kasuwanci?

  Malam Sulaiman: Ina kira ga masu wannan kasuwanci su rika tsayawa kan gaskiya, domin ita gaskiya ba a jin kunyarta. Don haka ina kira kan mu rika tsayawa kan gaskiya, mu rika bayar da abin da ya dace.

  Kuma ina kira  ga gwamnati ta  samar mana rijiyoyin burtsatse a wannan kasuwa. Domin muna amfani da wutar lantarki a wannan kasuwa, kuma muna fama da wannan matsala ta ruwa a wannan kasuwa, don haka akwai bukatar a sami ruwa a wannan kasuwa.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here