Gwamna Lalong Ya Amince Da Bai Wa ‘Yan Majalisa Da Sashin Shari’a ‘Yanci

0
337
Dokta Makut Simon Macham Kakakin gwamnan Jihar Filato

Isah Ahmed Daga Jos

GWAMNAN jihar Simon Lalong ya amince da dokar bai wa ‘yan majalisun jihohi da sashin shari’a ‘yancinsu ta fanni kudi, da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu. Kakakin Gwamnan Dokta Makut Simon Macham ne, ya bayyana haka a zantawarsa da wakilinmu a garin Jos.

Ya ce a matsayin Gwamna Lalong na mai bin doka da oda, na kundin tsarin mulkin Najeriya, tuni ya amince da wannan doka ta bai wa ‘yan majalisar jiha da sashin shari’a ‘yanci ta fannin kudi.

Ya  ce don haka tuni gwamnan ya fara shirye shiryen aiwatar da wannan doka, ta hanyar kafa kwamitoci da za su ba shi shawara kan wannan al’amari.

Ya ce da zarar wadannan kwamitoci da ya kafa sun gama aikinsu sun mika masa rahotonsu, zai fara aiki da wannan doka,  ba tare da bata lokaci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here