Jirgin Sama Na Farko Ya Tashi A Sabon Filin Jirgin Saman Kasa Da Kasa Na Yobe.

1
936
Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
A kokarin da gwamnatin jihar Yobe ke yi don ganin an samar da hanyoyin sufuri na zamani don jihar ta yi kafada da kafada da sauran jihohin kasar nan jirgin sama na farko ya fara tashi a sabon  filin jirgin saman daukar kaya nna kasa da kasa da ke Damaturu da gwamnatin ta gina.
A karshen makon da ya gabata ne Gwamnan jihar Alhaji Mai Mala Buni ya jagorancin wasu jiga-jigan ahugabannin jihar da kuma babban Kwamandan mayakan saman kasar nan da sauran jami’an rundunar don gane wa idonsu yadda jirgin farko zai fara tashi a wannan sabon filin jirgin sama da tsohuwar gwamnatin Alhaji Ibrahim Gaidam ta fara ginawa a shekarar 2017.
A wannan rana ne dai wasu jiragen da suka kunshi na mayakan kasar nan mai lamba NAF 961, ya sauka da wajen misalin karfe 1.59 na rana sai kuma wani jirgin sama na biyu mai lambar N100EK, da ke dauke da magungunan masu dauke da cutar COVID-19 a matsayin gwaji.
Gwamna Mai Mala Buni da ya jagoranci wannan biki ya yi matukar nuna farin cikinsa dangane da wannan aiki na filin jirgi musamman dangane da kammaluwarsa.
A cewar Gwamnan kokarin kammaluwar wannan aiki babban abin fahari gare shi musamman kan alkawarin da gwamnatinsa ta dauka kan kokarin kammala aikin a kan lokaci.
Wannan aiki na gina wannan filin jirgi gwamnatin da ta shude ne ta ba da shi watan Satumba na 2017 lokacin tsohon Gwamna Sanata Ibrahim Gaidam.

1 COMMENT

  1. Muma yan TARABA muma muku murna da Allah yasa aka kammala muku wannan aiki nafilin jirgin sama Allah yasadaku da alkairin dakecisa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here