Majalisa Ta Amince Wa Buhari Cin Bashin Dala Biliyan 5

0
288

Rahoton Z A Sada

MAJALISAR dattawan Najeriya ta amince wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbo rancen kudi dala biliyan 5.513.

Majalisar ta amince da buƙatar ne a zaman da ta yi jiya ranar Talata, ƙasa da mako ɗaya da shugaban ya tura da buƙatar karbo rancen daga waje domin cike giɓin kasafin kudin 2020.

Bayanai sun ce Najeriya za ta karɓo rancen ƙudin ne daga hukumar lamuni ta duniya IMF da Bankin raya ƙasashen Afirka da Bankin duniya da kuma Bankin musulunci.

A makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya aika wa majalisar da kasafin kuɗin na sama da tiriliyan10 da aka yi wa kwaskwarima

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here