Zargin Shugaban Majalisar Dattawa Da Fifita ‘Yan Kabilarsa Ba Gaskiya Ba Ne..in ji Sani Fema.

0
353
Muhamnad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
BABBAN mashawarci na musamman ga shugabaan majalisar dattawa na kasa  kan harkokin wasanni Alhaji Sani Fema ya karyata zargin da wata kungiya wai daga yankin arewa maso gabas ta yi wai kan cewar, shugaban majalisar ta dattawa Sanata Ahmad Lawan wadda dan jihar ta Yobe ne na fifita ‘yan kabilarsu ta Bade a duk wata dama da aka ba shi na daukar aiki ko mashawarta da masu taimaka masa a ofishinsa kan gudanuwar aiki fiye da duk dan wani yanki a jihar.
Alhaji Sani Fema ya fadi hakan ne a tattaunawrsa da wakilinmu ta wayar tafi da gidan ka jim kadan da wannan kungiya mai suna North-East door to door campaign organization for PMB ta harshen turanci ta ambata haka ne ta bakin Shugabanta na shiyya Komred Aliyu Bala a cikin wata jaridar da ba wannan ba.
Mai ba da shawara ga shugaban majalisar dattawan ya ci gaba da cewar, wannan magana da wannan kungiya ta yi ba gaskiya ba ne kwata-kwata Kuma ma hasali ma ai sun yi hakan da wata manufa ne.
Alhaji Sani Fema ya ci gaba da cewar, wannnan zargi da wannan kungiya ta yi shi a saninsa kuma ya hakkake wasu daga cikin shugabanninta ne ake so amfani da su don cimma wata manufa amma ba dukkanin ‘yan kungiyar ba.
Ya ci gaba da cewar, ai da yawa-yawan mutanen da shi shugaban majalisar dattawan ya nada masu ba shi shawara da mataimakansa aksarinsu ba daga mazabarsa suke ba,
A cewarsa, “kamar ni Sani Fema da shugaban majalisar dattawan ya nada a matsayin babban mai ba shi shawara da taimaka masa a bangaren ci gaban wasanni na fito ne daga karamar hukumar Fune a mazabar majalisar dattawan kudancin Yobe, to ai ka ga tun nan ba gaskiya ba ne wannan magana, kuma bayan ni akwai wasu da yawa da suka fito daga bangarori da dama na jihar ta Yobe da ma wasu bangarorin kasar nan da shugaban ya ba su matsayi a ofishinsa”.
Don haka ne sai ya ja hankalin masu wannan zargi da kar su ba da kofa wasu na amfani da su son wata nummumar manufarsu, domin kuwa shugaban majalisar dattawan mutum ne da ke daukar duk wani dan Jihar Yobe tamfar uwa daya uba daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here