‘Ƴan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutum 70 A Zamfara

0
995

Rahoton Z A Sada

RAHOTANNI daga jihar Zamfara a Najeriya na cewa wasu gungun ‘yan bindiga sun kashe fiye da mutum 70 a wasu hare-hare da suka kai wasu kauyuka a ranar Talata da Laraba.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun fara farwa mutanen kauyukan ne a ranar Talata inda suka kashe mutum 15.

Haka zalika ‘yan bindigar sun sake farwa mutanen yayin da ake yin jana’izar waɗanda aka kashe sa’annan ‘yan bindigar suka kashe mutum 50.

Abin ya faru ne a kauyukan Gidan Ƙane da Tungar Mawa da ‘Yar Gada da kuma wasu sauran kauyuka.

Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan da aka kai wa harin Kabiru Musa ya shaidawa BBC cewa mazauna ƙauyukan na cikin zaman ɗar-ɗar.

Ya shaida cewa ‘yan bindigar sun zo ƙauyukan kan babura fiye da 100 yayin da suka kai harin inda suka yi goyon uku-uku.

Ya bayyana cewa gawarwakin da ake yi wa jana’iza tun a farko dole aka bar su a yashe saboda babu yadda za a yi a ci gaba da jana’izar.

BBC ta tatattauna da kwamishinan tsaro na jihar Zamfara Abubakar Muhammad Dauran inda ya tabbatar da kashe mutum 21 a halin yanzu, sai dai ya ce ana nan ana bincike kan asalin yawan mutanen da aka kashe,.

Ya kuma bayyana cewa akasarin ɓarayin da suka kai harin sun gangaro ne daga jihar Katsina sakamakon fatattakarsu da ake yi kamar yadda suka samu rahoto.

Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ‘yan bindiga suka addaba. A kwanakin baya dai, an samu sauƙin kai hare-haren, sai dai a halin yanzu abubuwan na neman ƙara sukurkucewa sakamakon yawan hare-haren ƴan bindiga.

A kwanakin baya dai, sai da dakarun rundunar Hadarin Daji ta sojojin Najeriya suka kashe ‘yan bindiga da dama a jihar ta Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here