Akwai Yiwuwar A Gudanar Da Hajjin Bana, Saudiyya Muke Saurare – Hukumar NAHCON

0
720

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN hukumar jin dadin alhazan Najeriya, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya ce hukumar na sauraron matsayin kasar Saudiyya ne kafin ta sanar wa ‘yan Najeriya ko Hajjin bana zai yiwu.

Ya ce akwai yiwuwan gu danar da Hajjin bana duk da tsoron da cutar Coronavirus ta jefa cikin zukatan al’umma.

Amma idan haka ya yiwu, zai zo da wasu matakai masu tsaurin gaske domin karin lafiyan Mahajjata.

Ya ce idan haka ya faru, da yiwuwan a rage adadin maniyyatan kasashe.

A jawabin da mataimakin diraktan labarai na hukumar NAHCON, Mousa Ubandawaki, ya saki, ya ruwaito Hassan da bayyana hakan ne hirar yanar gizon da kungiyar kamfanonin safarar maniyattan Najeriya.

Yace: “Gwamnatin kasar Saudiyya kadai ce za ta iya yanke shawara ta karshe. Duk abinda zamu yanke na dangane da abin da Saudiyya ta yanke.”

Yace da yiwuwan kasar Saudiyya ta amince a gudanar da Hajjin bana saboda matakan da take dauka wajen hana yaduwar cutar COVID-19 da kuma adadin masu samun waraka a kasar kullum.

Daga cikin alamun Hajjin bana zai gudana da ya hararo sune bude Masallatai, sassauta dokokin hana fita, sanya na’urorin tsaftace jiki a kofofin shiga Masallatau da kuma adadin masu waraka daga cutar a kulli yaumin.

Sauran alamun sune raguwar adadin masu kamuwa da cutar a kasar da kuma bude sabbin dakunan gwaji shida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here