Ana Ta Zubar Da Kalamai Kan Bashin Da Gwamnatin Buhari Ke Ciyo Wa Najeriya

0
384

Rahoton Z A Sada

SAMAR da yunƙurin da gwamnatin Buhari ke yi na karɓar rance a gida da wajen Najeriya domin aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2020 ya haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar.

A ranar Talata ne majalisar dokokin Najeriya ta amince da buƙatar da shugaban ya aika mata ta karɓar rancen fiye da dala biliyon biyar bayan a watan Afrilu majalisar ta amince ya karɓo rancen naira biliyan 850 daga cikin gida.

Gwamnatin APC ta shugaba Buhari ta ce za ta yi amfani da kuɗaɗen da za ta karɓo rancen biliyoyin daloli ne domin cike gibin kasafin kuɗin musamman yadda annobar korona ta katse mata hanzari da kuma ƙalubalen da Najeriyar ke fuskanta ta fuskar kudin-shiga, sakamakon faɗuwar farashin mai a kasuwannin duniya.

Amma babbar jam`iyyar adawar kasar da wasu masana na sukar yawan rancen na shugaban wanda suke cewa yana tattare da hatsari ga makomar ƙasar.

PDP ta yi zargin cewa bashin da gwamnatin APC ke ci ya wuce kima – zai iya jefa Najeriya cikin wahala, kamar yadda Mista Kola Olabongdiyan sakataren yaɗa labaran jam`iyyar ya shaida wa BBC.

“Ƴunkurin Buhari na sake karɓar bashin sama da dala biliyan biyar, bayan sama da Dala Biliyan 22 da miliyon 79 da ya yi niyyar karɓa da farko don aiwatar da kasafin kudin shekara ta 2020 ba tare da wani ƙwaƙƙwaran shirin biyan bashin ba, zai rage ƙimar kasarmu,” in ji shi.

Mista Olabongdiyan ya kara da cewa yawan bashin da Najeriya ke karba zai buɗe ƙafa ga hukumomin da ke ba da rance na ƙasashen waje su mamaye bangarorin tattalin arzikin ƙasar.

Jam`iyyar PDP dai na fargabar cewa gwamnatin APC na ƙoƙarin jefa Najeriya cikin halin tsaka-mai-wuya ta hanyar mayar da ƙasar tamkar baiwa irin ta zamani, kasancewar ta sarayar da makomar ‘yan Najeriya, ta yadda wasu hukumomin ƙasashen waje za su kafa musu ƙahon-zuƙa!”

Amma jam`iyyar APC mai mulkin Najeriyar ta ce bashi hanji ne yana cikin kowa, tun da hatta manyan ƙasashen duniya kan karɓi rance don raya ƙasa.

APC ta ce karɓo rancen ba laifi ba ne, kamar yadda Alhaji Ibrahim Masari babban jami`in walwalar jam’iyyar na kasa, ya shaida wa BBC, yana mai cewa “matuƙar za a yi abin da ya dace da bashin ba laifi ba ne.”

“Kamata ya yi ‘yan adawa su sa ido idan har adawar za su yi su ga abin da aka ce za a yi da bashin da za a ciwo idan ba a yi ba sannan suke da bakin magana,” in ji shi.

Wasu masana tattalin arziki a Najeriya, irin su Dokta Shamsuddeen Muhammad malami a jami`ar Bayero ta Kano na dasa ayar tambaya a kan hanzarin da gwamnati ke kawowa wajen karɓar rancen.

Dokta Shamsudden ya ce a jimlace ƴan kwanakin nan bashin da gwamnatin APC ta ke shirin karɓa ya haura naira tiliyan 5. Kuma ba ya wuce naira tiliyan biyar zuwa shida a shekara na kudaden shiga da Najeriya ke samu.

“A kasafin kudin 2020 kusan naira tiriliyan uku zai tafi ne a bashi. kusan kashi 30 cikin 100 zai tafi ne a biyan bashi. Kuma ana bin Najeriya bashin kusan naira tiliyan 28,” in ji shi.

Masanin ya yi gargadin cewa idan bashi ya yi yawa durkusar da kasa yake yi maimakon farfado da ita.

Ga alama za a ci gaba da tabka muhawara a kan rance da gwamnatin shugaba Buhari ke karba.

Wasu na ganin cewa maimakon cin bashi don cike giɓin kasafin kuɗi, kamata ya yi gwamnati ta taƙaita kasafin kuɗin daidai ruwa daidai gari, yayin da wasu kuma ke ganin sai an hada da rance za a farfado da tattalin arzikin kasar.

Wasu kuma na bayyana damuwa kan yadda idan an karɓi rancen da wuya a ji duriyarsa, duk kuwa da shaidar da aka yi wa shugaban kasar ta gudun duniya da kyamar cin hanci da rashawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here