
Isah Ahmed Daga Jos
DAN majailasar dokoki ta Jihar Bauchi, mai wakiltar mazabar Lame da ke Karamar Hukumar Toro, Honarabul Bala Abdu Rishi ya tallafa wa marayu da gajiyayyu na mazabarsa, da kayayyakin sawa da abinci. Dan majalisar ya tallafa wa marayu da gajiyayyun ne, a garin Rishi da ke mazabar.
Da yake zantawa da wakilinmu bayan kammala rabon kayayyakin tallafin, Dan majalisar ya yi bayanin cewa a wannan tallafa wa marayu, ya tallafa wa marayu 250, da kayayyakin sawa.
Ya ce a wannan tallafin marayu, ya fi mayar da hankali ne ga marayu qananan yara da aka mutu aka bari musamman mata, domin su ne abin tausayi.
‘’A kowanne lokaci ana yi wa yara tanadin kayan da za su sanya a ranar Sallah. Don haka yara marayu suna shiga wani mummunan yanayi, a wannan lokaci na Sallah. Saboda haka muke kula da irin wadannan yara marayu, wajen bayar da wannan tallafi’’.
Dan majalisar ya yi bayanin cewa tun lokacin da yake aikin gwamnati, yake tallafa wa marayu. Don haka a duk shekara, yana gudanar da irin wannan aiki na tallafa wa marayu. Domin tallafa wa maraya, abu ne mai lada a wajen Allah.
Ya ce rashin kula da marayu, yana daya daga cikin abin da yake kawo matsalar rashin kwanciyar hankali a kasar nan, don haka ya yi kira ga masu hali su rika tallafa wa marayu da gajiyayyu.
Dan majalisar ya ce a watan Azumin da ya gabata, ya sayi gyero da buhun shinkafa 60, ya raba wa mabukata 200, a wannan mazaba.