Sule Lamido Zai Iya Warware Matsalolin Najeriya-Nafi’u Jos  

  0
  957
  Alhaji Nafi’u Ya’u Jos

  Isah Ahmed Daga  Jos

  SHUGABAN kungiyar matasa ta yakin neman zaben shugaban kasar da ya gabata, ta tsohon Gwamnan Jihar Jigawa  Alhaji Sule Lamido  na yankin jihohin arewa ta tsakiya.  Alhaji Nafi’u Ya’u Jos,  ya bayyana cewa babu shakka idan al’ummar Najeriya suka zabi Alhaji Sule Lamido, a matsayin shugaban Najeriya a zaben shekara ta 2023 mai zuwa, zai iya warware matsalolin da suke damun Najeriya. Alhaji Nafi’u Ya’u Jos ya bayyana haka ne, a lokacin da yake jawabi a wajen taron walimar murnar cika shekara 5, da saukar Alhaji Sule Lamido daga kujerar Gwamnan Jihar Jigawa, da kungiyar ta shirya a garin Jos.

  Ya ce halin da Najeriya ta shiga  tana neman taimakon mutane irin su Sula Lamido ne. Don haka idan Allah ya bai wa Sule Lamido, shugabancin kasar nan za a sami waraka.

  ‘’Babban abin da yasa har yanzu muke tare  da shi,  shi ne shugabancin Najeriya yana bukatar mutum mai basira da hangen nesa da tausayi da kishin kasa. Kuma dukkan  wadannan abubuwa Alhaji Sule Lamido yana da su’’.

  Alhaji Nafi’u Ya’u ya yi bayanin cewa idan aka koma kan jam’iyyarsu ta PDP,  Alhaji Sule Lamido shi ne  cikakken dan jam’iyyar PDP,  domin tun da aka kafa wannan jam’iyya da shi, bai taba ficewa zuwa wata jam’iyya ba.

  Ya yi kira ga al’ummar Najeriya su daina cewa ba zasu sake yin zabe ba, saboda abubuwa marasa dadi da gwamnatin APC tayi masu.

  Ya bukaci su yi hakuri su gyara kuru’unsu, su fito su zabi wanda suke so a zaben shekara ta 2023 mai zuwa.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here