ABUTH Shika Ta Fara Cika Da Masu Cutar Korona – Masarautar Zazzau

0
324

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

MASARAUTAR Zazzau a jihar Kaduna ta koka kan tashin gwauron zabo da adadin masu cutar Coronavirus ke yi a cibiyar kulawar da ke asibitin koyarwa na jami’ar ABU, Shika Zariya.

Yayin da yake magana a wata ganawar wayar a Zariya. Salanken Zazzau kuma shugaban kiwon lafiyar masarauta, AbdulKadir Salanke, ya ce cibiyar ta fara cika saboda karuwar masu cutar da ake samu a Masarautar.

A cewarsa, mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris. ya gayyaci dakatai ne da shugabannin addini zaman wayar da kan ne saboda sun fi kusa da a’l’umma kuma zasu taimaka wajen yada sakon.

Ya yi kira ga jama’ar Zazzau su bi umurnin hukumomin kiwon lafiya domin takaita yaduwar cutar saboda gaskiya ce kuma tana daukar rayuka.

Salanke ya mika godiyar masarautar ga gwamnati bisa hadin kai wajen samar da cibiyar killace masu cutar COVID-19 mai daukar mutane 20 a ABUTH.

A bangaren gwamnati kuwa, mataimakin diraktan hukumar cigaban kananan asibitoci, Hamza Ikara ya ce cutar COVID-19 ta yadu a kananan hukumomin jihar guda tara yanzu.

Sun hada da Igabi, Chukun, Kaduna ta Arewa , Kaduna ta kudu, Zariya da Sabon Gari, Soba, Giwa da Makarfi.

Ikara ya ce an zabi gudanar da taron a Zariya ne saboda ita ce hedkwatar masarautar Zazzau wacce ta kunshi kananan hukumomi 8 cikin 9 da aka ambata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here