An Tuɓe Shugabannin Kananan Hukumomi 14 A Zamfara

0
825
Rabo Haladu Daga Kaduna
MAJALISAR Dokokin Jihar Zamfara ta sauke shugabannin ƙananan hukuma 14 bayan wata ganawar gaggawa sannan ‘yan majalisar suka nemi Gwamna Bello Matawalle ya naɗa kantomomi.
Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Shamsudden Mafara ne ya sanar da hakan bayan kammala zamansu a yau Juma’a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai.
Shamsudden Mafara ya ce a cikin shawarwarin da suka bai wa Gwamnan sun buƙaci a gudanar da zaɓe a ƙananan hukumin da abin ya shafa cikin wata uku masu zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here