Gwamnatin Jigawa Za Ta Sanya Almajirai 1322 Da Aka Dawo Mata Da Su A Makarantu

0
440

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN jihar Jigawa ta ce za ta saka almajirai 1,322 makarantu bayan an dawo mata da su jihar sakamakon barkewar annobar korona a jihohin kasar nan.

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a kan annobar korona a ranar Laraba a garin Dutse.

“Kamar yadda na bayyana a jawabi na na baya, an dawo wa jihar Jigawa da almajirai 1,322 daga jihohi daban-daban. Mun kula da su kuma muna samar musu da kayayyakin more rayuwa.

“Mun mika dukkan almajiran hannun iyayensu ban da 23 daga ciki da ke dauke da cutar coronavirus amma suna karbar magani a cibiyar killacewa.

“Mun ba da umarnin saka yaran a makarantar firamare tare da ci gaba da ba su ilimin Qur’ani,” Badaru ya ce.

Gwamnan ya ce, a halin yanzu jihar na samun nasarar yakar cutar coronavirus saboda yanzu yawan masu cutar na raguwa.

Ya ce sabbin masu cutar a jihar, an gano cewa wadanda suka yi mu’amala da masu cutar ne da farko.

Ya ce wannan ci gaban na bayyana cewa gwamnatin jihar na yin nasarar yaki da cutar don haka za ta sabunta yanayin yakin.

“Amma kuma, masu cutar za su ci gaba da raguwa matukar mun bai wa gwamnati goyon baya tare da kiyaye dukkan dokokin hana yaduwar kwayar cutar.

“A yayin da muka sassauta tare da ajiye dokar kulle a gefe, dole ne mu kiyaye yin nesa-nesa da tsafta da kuma amfani da takunkumin fuska a yayin da ake shiga cikin mutane.

“Duk wani abu da bai kai wadannan matakan ba, zai iya kawo yaduwar cutar,” Badaru ya ja kunne.

Gwamnan ya bayyana cewa, ana ci gaba da kokarin kammala cibiyar killacewa mai gado 450.

Kamar yadda ya ce, idan masu cutar suka ci gaba da raguwa, jihar ba za ta kai hasashen da kwararru suka yi ba.

“Na yi alkawarin gaggauta kammala ginin cibiyar killacewa mai gado 450 a jihar. A halin yanzu ana ci gaba da aiki.

“Idan muka ci gaba a haka, ba za mu kai hasashen da kwararru suka yi ba na cewa za a kai 800 a yawan masu cutar.

“Duk da haka, za mu cika alkawarinmu,” Badaru ya tabbatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here