Ta Yi Wa Kishiyarta Wanka Da Tafasasshen Ruwan Zafi

0
335

Daga Usman Nasidi.

WATA mata ‘yar shekara 26 a unguwar Zango da ke birnin Kano, Zulaihat Nasir, ta ji wa kishiyarta, Nafisa Isa, mumunan rauni bayan yi mata wanka da ruwan zafi.

A labarin da majiyarmu ta samu, na bayyana cewa Nafisa da Zulaihat na zaman aure ne gidan Ibrahim Sabo, mazaunin jihar Kano.

Rahoton ya bayyana cewa wacce aka watsa wa ruwan zafin ta ji raunin kuna a kai da kirji kuma an garzaya da ita asibitin Abdullahi Wase.

Zulaihatu wacce ta aikata wannan laifi ta yi bayani a ofishin yan sanda cewa kishiyarta ce ta fara kulleta cikin daki kuma ta yi barazanar banka mata wuta.

Ta ce ta yi mata wanka da ruwan zafi ne matsayin ramuwar gayya kan kulleta da barazanar da ta yi mata.

Ta ce: “Mun yi fada da ita ne, amma da na koma dakina, sai ta kulle kofar ta garkame ni ciki tana barazanar banka min wuta cikin dakin.”

“Tun karfe 4 na yamma da ta kulle ni cikin dakin har Magariba da Maigidanmu ya dawo gida.”

“Saboda haka na fusata kuma na yanke shawarar daukar fansa ta hanyar zuba mata ruwan zafi.”

Amma yayin da jami’an ‘yan sanda ke yi mata tambayoyi, ta bayyana nadamarta kan abin da ta aikata.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da labarin ya ce ya faru ne ranar Lahadi, 31 ga Mayu misalin karfe 11 na safe.

Ya ce kwamishanan ‘yan sandan jihar, Habu Sani, ya ba da umurnin mayar da lamarinta ofishin sashen CID domin bincike mai zurfi.

Ya kara da cewa idan aka kammala binciken, za a caji duk wanda aka kama da laifi zuwa kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here