An Raba Wa Mutum 2000 Kayan Abinci Na Tallafin Korona A Karamar Hukumar Lere

0
717

Isah Ahmed Daga Jos

AN raba wa sama da mutum dubu 2, kayayyakin abinci   na tallafin Kurona,  a Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, a karshen makon da ya gabata. Shi dai wannan kayayyakin abinci da ya hada da  shinkafa da Alkama da wake da taliya da garin Samanvita da man girki. Gwamnatin Jihar Kaduna ce, ta tura  Karamar Hukumar ta Lere, karkashin wakilcin  Daraktan hukumar samar da ruwa ta Jihar Kaduna ta RUWASA, Injiniya Ahmed Manur.

Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan tallafin kayan abinci, Wazirin Saminaka Alhaji Muhammad Rabi’u Umar, ya bayyana cewa gaskiya gwamnatin Jihar Kaduna ta yi abu mai kyau, kan wannan tallafin kayan abinci da ta kawo karamar hukumar Lere.

Ya mika  godiya ga Daraktan Hukumar ruwa ta jihar Kaduna, Injiniya Ahmed Manir kan yadda ya tsaya wajen ganin an raba  kayan, kamar yadda ya kamata.

Ya  yaba wa al’ummar  karamar hukumar, kan yadda suka yi biyayya ga dukkan matakan kare wannan cuta ta Kurona,  da gwamnati ta sanya.

  • Wasu mata da suka sami tallafin kayan abinci na Kurona a Karamar Hukumar Lare.

Shi ma da yake zantawa da wakilinmu wani babban dan kasuwa, Alhaji Ahmadu Yahaya Saminaka ya bayyana cewa babu shakka Gwamnan jihar Kaduna.  Ya bayar da wannan tallafi ta hanu nagari, wanda ya  isar zuwa  ga mutanen da suka kamata.

Ya ce an kai wannan tallafi zuwa ko’ina a karamar hukumar,  kuma jama’a sun yi farin ciki, don haka ya yi  godiya ga Gwamnan.

A zantawarsa da wakilinmu kan wannan al’amari,  Talban Saminaka Alhaji Musa Mudi ya bayyana cewa wannan kayan abinci da aka kawo ta haunu Injiniya Ahmed Manur, ya yi kokari wajen raba kayan  kamar yadda ya kamata.

Ya ce wannan kaya da aka rabawa kungiyoyi  da talakawa da gajiyayyu  a lungu da sako na karamar hukumar,  ya kai  sama da mutum dubu 2.

A  zantawarsa da wakilinmu daya daga cikin jami’an da suka raba wannan kaya, Alhaji Bature Hassan Saminaka, wanda ya kula da bangare tsofaffi da gajiyayyu na rabon kayan ya bayyana cewa sun shiga kauyuka da dazuzzuka na karamar hukumar.   Sun rabawa tsofaffi da  gajiyayyu mutum 600 wannan kayan tallafi, batare da banbancin  siyasa ko addini ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here