An Yi Zanga-zanga Kan Rashin Tsaro A Katsina

0
397
Rabo Haladu Daga Kaduna
MAZAUNA kauyen ‘Yantumaki da ke jihar Katsina  sun gudanar da zanga-zanga kan tabarbarewar tsaron da yankin ke fama da shi.
Hotunan intanet sun nuna masu zanga-zangar da safiyar yau Talata sun hau kan tituna suna kokawa kan yadda gwamnatocin tarayya da na jihar suka bar matsalar rashin tsaron tana ci gaba da tabarbarewa.
Bayanai sun nuna cewa matasan yankin sun harzuka ne bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen da jijjifin ranar Talata inda suka sace wani malamin asibiti da diyarsa. Koda yake babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar wa manema labarai  hakan.
Matasan sun rika kona tayoyi da kuma allunan jam’iyyar APC mai mukin jihar don nuna rashin jin dadinsu game da rashin tsaron.
Ko a watan jiya sai da wasu mazauna yankin karamar hukumar Jibia suka yi zanga-zanga domin nuna matukar bacin ransu game da halin ko-in-kula da suke zargi shugabanninsu suna yi kan batun tsaron jihar.
Matsalar tsaro na c gaba da ta’azzara a arewa maso yammacin Najeriya a baya baya nan.
Kungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutane fiye da dubu takwas a rikicin arewa maso yammacin kasar cikin shekaru 10 .
Hukumomi dai suna cewa suna daukar matakan shawo kan matsalar, amma masu lura da lamuran tsaro sun ce akwai bukatar a dauki karin matakai domin magance ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here