Najeriya Ta Ba Da Hutun Kwana Daya Na Ranar Dimokuradiyya

0
372

Rahoton Z A Sada

GWAMNATIN Tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Juma’a 12 ga watan Yuni a matsayin hutu na Ranar Dimokuraɗiyya ga ma’aikata.

Sanarwar da Sakatariya a ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar, Georgina Ehuriah a madadin Minista Ogbeni Rauf Aregbesola, ta ce ministan ya taya ‘yan Najeriya murnar ɗorewar mulkin dimokuraɗiyya.

Wannan ne karo na uku da za a yi bikin Ranar Dimokuraɗiyya ranar 12 ga watan Yuni tun bayan da Shugaba Buhari ya sauya ranar daga 29 ga watan Mayu a ranar 6 ga watan Yunin 2018.

Ministan harkokin cikin gida ya shawarci ‘yan Najeriya da su ci gaba da bin umarnin masana harkar lafiya domin kare kansu daga annobar korona, wadda zuwa yanzu ta yi ajalin mutum 354 sannan ta kama 12,486 a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here