Almajiran 33 Da Aka Kawo Daga Kaduna Zuwa Sokoto ‘Suna Dauke Da Cutar’Korona

0
345
Rabo Haladu Daga Kaduna
JIHAR Sokoto ta bayyana cewa wasu almajirai 33 da aka kai jihar daga Kaduna ne suka sake kai cutar korona jihar.
Ma’aikatar lafiya ta jihar Sokoton ce ta wallafa haka a shafinta na Twitter inda ta ce almajiran sun taho ne tun daga Zaria ranar Alhamis, amma a halin yanzu an killace su a sansanin masu yi wa ƙasa hidima na jihar Sokoto.
Jihar ta bayyana cewa cikin almajirai 33 da aka yi wa gwajin cutar, 11 daga cikinsu na ɗauke da cutar ta korona. Ta kuma bayyana cewa za ta haɗa hannu da jihar Kaduna wajen ganin cewa an gano asalin wuraren da almajiran suka fito a cikin garin Zaria domin nemo waɗanda suka yi mu’amula da su.
Cutar ta korona dai ta sake ɓulla Sokoto ne a ƙasa da mako guda bayan jihar ta ayyana cewa duka masu korona da suka yi saura a jihar sun warke.
Jihar Zamfara ce ta farko da ta fara fitowa ta bayyana masu cutar a jihar sun warke sai Kebbi sa’annan Sokoto.
A ƙididdigar da hukumar NCDC ta fitar a ranar Asabar, an sake samun sabbin mutum biyu da suka kamu da cutar ta korona jihar Kebbi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here