Ba A Kula Da Mu Ba Tun Bayan Rasuwar Mahaifinmu — Iyalan Abacha

0
420

R Z A Sada

SHEKARU ashirin da biyu bayan rasuwar tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, Janar Sani Abacha, iyalansa sun bayyana yadda suke ji dangane da maraici.

Daya daga cikin ‘ya’yan marigayin, Sadiq Abacha, ya shaida wa BBC cewa alakarsu da wasu abokan mahaifinsu a yanzu tana ba su mamaki.

Sadik ya ce, “Kamar iyalan janar Babangida ana gaisawa ana kuma mutunci, haka iyalan shugaban kasa na yanzu Muhammadu Buhari suma ana gaisawa

Tsohon shugaban Najeriya Janar Sani AbachaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Ya ce idan sun hadu ana gaisawa a yi dan labari sannan a dan tuna da baya amma da iyalan janar Babangida ake hakan.

Sadik ya ce, a bangaren iyayen nasu kuwa a gaskiya sun zaci cewa bayan rasuwar mahaifin nasu za a dan jasu a jiki a rinka basu shawara ko makamancin haka, amma sam ba bu haka.

Ya ce ” Da mun zaci za a ja mu kusa, a kula da mu sannan a rufa mana asiri amma sai muka ga ba haka ba sam”.

Sadik ya ce ” A matsayina na dan marigayi Sani Abacha bana jin dadi a kan maganar kudade da ake yi, ba abune da zamu musanta muce ba a dawo da kudade ba, amma kuma kamar yadda kowa ke ji muma haka muke ji”.

Ya ce ” Akwai wasu manyan ‘yan siyasa da suka taka rawa a lokacin mulkin babanmu wadanda ke fitowa suke cewa kudin nan ba wai babbu su ba amma akwai dalilai da ya sa aka fitar dasu, amma duk wannan bayanin ba a ji sai batun an fita da kudi kawai”.

A bangaren batun sanya wa iyalan Abacha takunkumin fita zuwa kasashen waje, Sadik ya ce a lokacin da Yayale Ahmed na matsayin sakataren gwamnatin tarayya shi ya taimaka musu wajen ganin an dage musu takunkumin fitar.

Dan marigayi Sani Abachan ya ce,” Amma duk da haka har yanzu idan zanyi tafiya sai an tsare ni a filin jirgi an ce wai sunanmu na bakin littafi, kuma munje har wajen hukumar tsaro ta farin kaya sun bamu takardar shaidar cewa an cire sunanmu daga wannan littafin”.

Ya ce ” Ama duk da haka bata sauya zani ba, ko yaushe idan zan fita kona dawo daga wata kasa sai an tsareni, kuma baune ba wanda zan kai wa korafi a kai”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here