Ba Mu Zabi Shugabannin Najeriya Domin Su Kulle Mu Ba-Sheikh Jingir

0
534
Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ,

Isah Ahmed Daga Jos

SHUGABAN majalisar malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa al’ummar Najeriya basu zabi shugabannin Najeriya, domin su kawo masu dokar da za su kulle su a gidajensu ba. Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne, a lokacin da yake jawabi ga shugabannin kungiyar reshen Jihar Kaduna, da suka kawo masa ziyara, a garin Jos.

Ya ce mun zabi shugabannin Najeriya ne, bisa alkawarin za su kular mana da ‘yancin addininmu da tsaro da dukiyar kasa da bunkasa ilmi  da inganta aikin noma da kiwon lafiya da  gyara  hanyoyin kasar nan.

Ya ce a addinin  musulunci wannan alkawari ne shugabannin Najeriya suka yiwa al’ummar Najeriya. Kuma Allah ya ce a cika alkawari, domin kaya ne da za a tambayi, wanda ya yi  a ranar tashin alkiyama.

Sheikh Jingir ya yi bayanin cewa babu abin da zai sami musulmi, sai abin da Allah ya rubuta. Don haka duk yadda duniya ta juya,  babu abin da zai firgita shi

‘’Ni babu ranar da na jefa wa hukumar lafiya ta duniya kuri’ata, don ta zama shugaban Najeriya. Duk jama’a ta, babu ranar da muka yi haka.  Amma sai ga shi an kulle mu a gidajenmu, kamar  ‘yan kurkuku’’.

Ya  ce wannan mutuwa da ake tsoro duk inda mutum ya shiga a duniya, sai ta bi shi ta dauke shi.

Ya ce wannan mutuwa  wadda ba ganinta ake yi ba,  ta mayar da masana  kasa, domin ba su ganta ba, amma sun rufe jami’o’i da kwalejoji da kamfanoni da kasuwanni.

Ya ce Allah ya fara karbar addu’armu, domin yanzu kasashe da dama sun fara bude wuraren ibada, da kasuwanni da kamfanoni. Don haka mu ci gaba da rokon Allah, ya kubutar da duniya daga wannan matsala.

Tun da farko a nasa jawabin, Shugaban kwamitin ma’azin matasa na kungiyar reshen  Jihar Kaduna, Malam Aliyu Rashed Makarfi ya bayyana cewa tun da farko sun yi ta gwagwarmaya da mutane. Kan su fahimci wa’azin da Sheikh Sani Yahya Jingir  yake yi,  kan taudihi amma suka kasa fahimta. Sai yanzu da aka shiga  matsi,  suka fara gane gaskiyar al’amarin.

‘’Wadannan abubuwa da suke faruwa na  firgita al’ummar duniya, babu abin da zai same mu sai abin da Allah ya kaddara mana. Kuma addu’ar da muka rika yi kan wannan al’amari, shi ne ya kawo mana natsuwa’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here