Za A Biya Ma’aikatan Lafiya Kudin Allawus Kafin Karshen Mako – FG

0
332

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN tarayya, FG ta amince a biya ma’aikatan lafiya kudin allawus na musamman don hatsarin da suke fuskanta wurin yaki da annobar coronavirus na watanni biyu.

Chris Ngige, ministan kwadago da samar da ayyuka ne ya bayyana hakan yayin taron da aka gudanar tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da na kungiyar kwararrun ma’aikatan lafiya.

Ngige ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a biya kudaden allawus din ga ma’aikatan lafiyar ne saboda jajircewar suka yi wurin yaki da korona.

Za a biya kudaden allawus din na watannin Afrilu da Mayu ne kafin karshen wannan makon, a cewar ministan.

Ngige ya ce wannan matakin da aka dauka yana cikin yarjejeniyar da gwamnatin tarayya da wakilan ma’aikatan fanin lafiya suka cimma ne.

Ya kara da cewa gwamnatin ta kuma amince da samar da inshora ga maaikatan lafiya kamar yadda ya ke cikin yarjejeniyar da wakilan gwamnati da na kungiyoyin ma’aikatan lafiya suka ratabba hannu a kai a watan Afrilu.

“Mun gama bita baki daya, mun amince a bawa wannan jaruman maaikatan abinda ya dace a biya su saboda muhimman aikin da suke yi na kare mu baki daya.

“Mun tsayar wa kanmu da lokaci zuwa karshen wannan makon, maaikatan lafiya da ke aiki na yaki da annobar COVID-19 za su samu kudaden allawus dinsu na watannin Afrilu da Mayu kafin karshen mako.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here