An Sallami Wasu Malaman Jami’ar Bayero Saboda IPPIS

0
352

Daga Usman Nasidi.

JAMI’AR Bayero da ke Kano, BUK, ta sallami wasu malamanta biyar da aka dauka wucin gadi saboda dokar gwamnati tarayya na shiga tsarin biyan albashi na IPPIS da bai bayar da daman daukan malamai na kwangila ba

Da ya ke tabbatar da lamarin, Shugaban BUK, Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya ce jami’ar ta ba wa malaman da abin ya shafa wa’adin kwanaki 40 a maimakon 30 kafin sallamarsu daga aiki.

Shugaban jami’ar ya ce an da uki matakin ne domin biyaya ga tsarin biyan albashi na IPPIS da ya ce a dena biyan malaman da aka dauka na wucin gadi a lokacin da ainihin malaman makarantan suka shiga tsarin na IPPIS.

“Yana daga cikin sharrudan shiga tsarin biyan albashi na IPPIS. Kuma gwamnatin tarayya ta fayyace mana cewa sai dai idan jami’ar za ta iya biyan su daga kudin shigar ta kuma a yanzu ba za mu iya biyansu ba,” in ji shugaban.

Mista Yahuza Bello ya ce sallamar malaman na wucin gadi ba zai kawo cikas ga jami’ar ba duba da cewa tana da malamai kimanin 1,776.

Ya kara da cewa korar bai shafi ma’aikatan kwangilar da ba yan kasa ba.

Daya daga cikin malaman kwangilar da abin ya shafa, Dakta Saidu Dukawa, tsohon shugaban Hukumar Hisbah ta Kano ya tabbatar wa majiyarmu da batun a ranar Alhamis.

Ya yi karin bayani cewa jami’ar ta sanar da shi cewa za dakatar da kwangilarsa na aikin koyarwa na shekaru bakwai domin dokar gwamnati na shiga tsarin biyan albashi na IPPIS.

Mista Dukuwa ya ce, “Na shafe shekaru bakwai ina aiki a matsayin ma’aikacin wucin gadi a kuma duk shekaru biyu ake sabunta kwangilar. Dama shekara mai zuwa za a sabunta kwangila amma an soke jiya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here