Gobe Juma’a Shugaba Buhari Zai Yi Wa ‘Yan Najeriya Jawabi

0
375

Daga Usman Nasidi.

SHUGABA Muhammadu Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi gobe Talata, 12 ga watan Yuni, 2020 misalin karfe 7 na safe.

Buhari zai yi jawabin ne domin murnar ranar Dimokuradiyya.
Hadimin Buhari kan kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

Ya ce : “Domin murnar ranar Dimokuradiyyan Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya ranar Juma’a, 12 ga Yuni, 2020 misalin karfe 7 na safe.”

“Ana kira ga gidajen talabijin da rediyo su yi tarayya a tashar NTA da FRCN.” Shekarun baya, an saba gudanar da bikin ranar dimokuradiya a ranar 29 ga watan Mayu na kowace shekara gabanin shugaba Buhari ya sauya ranar a shekarar 2018.

Buhari ya yi hakan ne domin karrama marigayi Moshood Abiola da babbar lambar yabon kasar ta GCFR, domin tunawa da zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

Gwamnatin tarayyar Najeriya, ta ayyana ranar Juma’a, 12 ga watan Yuni, a matsayin ranar hutun aiki domin gudanar da bikin ranar Dimokuradiyya ta wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya ayyana ranar hutun a madadin gwamnatin tarayyar kasar.

Ya na mai taya daukacin al’ummar Najeriya na nan gida da kuma wadanda suke ketare, murnar zagayowar wannan rana da aka sauya salon mulki daga hannu soji ya koma hannun farar hula.

Ministan ya jinjinawa gwarazan mutanen da suka taka rawar gani wajen sadaukarwar da ta tabbatar da komawa kan tsarin mulki na Dimokuradiya a kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here