Gwamnatin Filato Ta Janye Dokar Kulle Da Ta Sanya

0
383

 Isah Ahmed Daga  Jos

GWAMNAN Jihar Filato Simon Lalong ya bayyana cewa gwamnatin jihar, ta janye dokar kulle da ta sanya a jihar, a matakan da kare yaduwar cutar annobar Coronavirus da ta sanya, har sai yadda hali ya yi. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga al’ummar jihar ta gidajen rediyo da tilbijin, kan halin da ake ciki dangane a jihar kan wannan  annoba ta Coronavirus, a yammacin yau alhamis.

Ita dai wannan doka ta kulle da gwamnatin jihar ta Filato ta sanya, ada tana aikin ne a ranakun litinin da talata da laraba, kafin zuwan wannan lokaci da ta janye.

Gwamnan ya yi bayanin cewa gwamnatin  ta janye wannan doka ne, sakamakon fito da qa’idojin sassauta matakan kare yaduwar wannan annoba, da kwamitin  da shugaban kasa ya kafa ya fitar,  tare da kira ga gwamnatocin jihohi, su kula da wadannan matakai a jihohinsu.

Ya  ce don haka gwamnatin ta kira taron masu ruwa da tsaki, kan yaki da wannan annoba a jihar,  ta  shirya masu taron karawa juna sani kan yaqi da wannan annoba na yini 2. Inda   aka tattauna tare da bayar  da shawarwari kan yadda za a yaki wannan annoba, a jihar.

 Ya ce don haka gwamnatin jihar ta janye wannan doka, har sai yadda hali ya yi.

Gwamna Lalong ya ce a tsawon lokacin da aka dauka na bin matakan kare wannan annoba a jihar, an sami nasarar yiwa mutum 2,032 gwaji kan wannan annoba.

Ya ce a ckin waxannan mutane da aka yiwa gwajin an sami mutum 130, dauke da wannan cuta. An sallami mutum 99 bayan da suka warke,  a yayin da mutum 3  suka rasu. Ya zuwa yanzu kuma  akwai mutum 26, da suke kwance ana yi masu jinya.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here