Kungiyar ‘Yan Kasuwa Hadaka (Amalgameted) Ta Kaddamar Da Sababbin Shugabanninta A Garin Azare

0
515
Gwamnan Al'umma Bala Muhammad
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Azare
KUNGIYAR ‘yan kasuwa ta hadaka (Amalgameted) ta Jihar Bauchi reshen karamar Hukumar Katagum sun gudanar da taro don rantsar da sababbin shugabanninta da za su gudanar da ayyukan kungiyar na tsawon lokacin da aka kayyade musu.
Wannan taron kaddamar da sababbin shugabanni dai an gudanar da shi ne a babban dakin taro na NINAD da ke garin Azare tare da halartar manya-manyan shugabannin kungiyar na jiha da suka hada da shugabanta Alhaji Abdullahi Y. Muhammad  (CACF) da sakatarenta Malam Garba Garus sai mataimakin sakataren kungiyar Malam Nuhu Minka’ilu Umar.
Sauran sun hada da  mataimakin shugaban kungiyar na jiha Alhaji Rufa’i mai Yadi Azare sai shugaban kungiyar na shiyyar Katagum Malam Kabiru Jadori Gamawa da sauransu, Akwai kuma Shugaban riko na karamar hukumar Katagum Alhaji Babayo Sunusi sai mai wakiltar mai martaba Sarkin Katagum Makaman Katagum Alhaji Ali Hussaini da sauran manyan baki.
Da yake rantsar da sababbin shugabannin  Barista Sani Muhammad DanLiti ya umarci kowannensu ne da ya daga hannunsa sama tare da ambata dukkan abin da ya fada. A karshe sababbin shugabannin sun yi rantsuwar kama aiki kamar yadda yake a dokar kada da kuma dokar kungiyar.
A bayaninsa na maraba da baki kodinetan kungiyar na Karamar Hukumar Katagum Malam Bala Moyi yabawa ya yi dangane samun damar da shubannin kungiyar na jiha suka yi tare da sauran kodinetocin kungiyar daga dukkannin kananan hukumomin jihar 20 na halartar wannan rantsuwa tasu.
Daga nan sai kodinetan ya ba da tabbaci kan cewar, cikin yardar Allah zai yi iya kokarinsa shi da sauran shugabannin kungiyar don ganin sun tafiyar da harkokin kungiyar cikin adalci da aminci.
Shi ma da yake jawabi shugaban kungiyar Hadaka na jihar Bauchi Alhaji Abdullahi Muhammad ya kalubalanci sababbin shugabannin ne da su yi adalci a yayin tafiyar da jagorancin su kuna su kuma ma su biyayya da goya baya ga gwamnatin jihar Bauchi karkashin Gwamna Bala Muhammad (Kauran Bauchi).
Shi ma mataimakin samataren kungiyar na Jiha Malam Nuhu Minka’ila Jan kunnen mambobin kungiyar  da su zama ma su biyayya ga kodinetocinsu kamar yadda ya kamata, tare da kauracewa nuna halin rashin da’a gare su.
Shi kuwa shugaban karamar hukumar Katagum Alhaji Babayi Sunusi a jawabinsa tabbaci ya bayar ga shugabannin kungiyar cewar a shirye yake don ba da goyon baya ta kowace fuska ga wannan kungiyar matuka.
A nasa jawabin mai wakiltar mai Martaba Sarkin Katagum makaman Katagum Alhaji Ali Hussaini Jan Kunne ya yi ga shugabannin kungiyar su zama ma su adalci ga kowa tare da bin dokokin kasa sau da kafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here