Ruwan Sama Mai Dauke Da Gagarumar Iska Sun Yi Sanadiyyar Rasa Rai Da Barnata Gidaje A Damaturu

0
414
Muhmmad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
RUWAN sama da iska mai karfin gaske da Allah SWT ya saukar a garin Damaturu fadar gwamnatin Jihar  Yobe a farkon. Wannan mako da muke ciki sun yi sanadiyyar rasa rai da jin munanan raunuka tare da rushewar gidaje masu tarin yawa.
Kamar yadda lamarin yake wannan ruwan sama mai dauke da iska mai karfin gaske an fara ne da misalin karfe 8.30pm na yammacin ranar itinin, kuma farin farko iskar ne ta fara sauka, aka shafe akalla mintuna goma ana yinta wadda a cikin mintunan da ba su wuce goma ba ne aka samu mafi yawan wannan barna ta rushewar gidaje da bishiyoyi masu tarin yawa kai ka ce ai iskar Tsunami ne ta afkawa wani yanki na wannan gari na Damaturu daga bisani ne kuma aka tsinke da ruwan saman da aka shafe kusan awanni biyu ana sheka shi kamar da bakin kwarya.
Wasu unguwannin da wannan iftila’i ya fi afkawa sun hada da Unguwar Nainawa, Fawari, Ajari Hausari, Kandahar Sabuwar Kasuwa, Pomfamari da Bindigari.
Wani mazaunin Unguwar Nainawa da wannan iftila’i ta rutsa da gidansa Malam Kamilu cewa ya yj in ba don ba a mamaki da ikon Allah ba, da dai ace wannan iska da ruwa da ban mamaki kasancewar a cewarsa cikin kasa da mintuna kimanin goma aka yi iska amma kuma ta’adinta na da ban mamaki, don kamar almara a cikin kiftawa saj kawai ya ga rufin kan dakunan sa an yi sama da su sai ga su a filin Allah.
Don haka ya roki gwamnatin Jihar Yobe da ta gaggauta kawo musu dauki, don samun yadda za su shimfida hakarkarunsu.
Har kai wa ga hada wannan rahoto dai ba a kai ga kammala hada alkaluman adadin gidajen da suka salwanta sanadiyyar wannna iftila’i na ruwan sama da iska.
Wata majiya na nuna cewar, wannan barnar ruwan sama da iska wasu kananan hukumomin Jihar da suka hada da karamar hukumar Tarmuwa, Bursari, Bade da Nguru su ma sun yi fama da hakan wadda rahoton ke nuna cewar, akalla mutane kimanin 7 ne suka rayukansu a rahoton da ba na hukuma ba.
Tunin dai Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ta bakin Darakta Janar na kafofin yada labarai da harkokin manena labarai nasa Alhaji Mamman Muhammad  ya  nuna alhininsa dangane da faruwar wannan lamari tare kuma da jajanta wa al’ummomin da ‘yan uwansu suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka samu raunuka tare da umurtar hukumar kai daukin gaggawa a jihar SEMA da ta gaggauta daukar matakin kula da wadanda suka ji raunuka don yi musu magani tare daukar alkaluman mutanen da wannan iftila’i ya rutsa da su.
Gwamnan ya kuma nemi hukumar ta SEMA da  ta kai daukin gaggawa ga al’ummomin don rage musu radadin wannan barna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here