Shin Majalisar Dattawan Najeriya ‘Yan Amshin Shata Ne Ga Shugaba Buhari?

0
523

Rahoton Z A Sada

A jiya Laraba 10 ga watan Yunin 2020 ne Majalisar Dattawan Najeriya ta tara ke cika shekara guda da fara aiki gadan-gadan.

Majalisar dattawan ta tara ita ce majalisar da shugabanninta suka fi na kowace majalisa ɗasawa da bangaren zartarwa a tsakanin nan sakamakon sun fito ne daga jam’iyya ɗaya da ta shugaban kasa, waɗanda kuma suka samu tubarrakinsa.

Ana ganin sakamakon dakan ɗaka, shikar ɗakan da aka yi wurin zaɓen shugabannin ne ya sa hakan ta faru.

Duk da cewa ɓangaren majalisa da na zartarwa kowanne zaman kansa yake, kuma sukan taka wa juna birki idan bukatar hakan ta taso, daya daga cikin ‘yan majalisar dattawan Sanata Yahaya Abdullahi ya bayyana cewa irin fahimtar da ke tsakanin shugabannin majalisar dattawa ta wannan jumhuriya da kuma ɓangaren shugaban ƙasa ta sa ba a jin kansu.

Sanata Yahaya ya ce su sun fi gaban ‘yan amshin shata, don a cikinsu ”akwai tsofaffin gwamnoni da ministoci da gogaggu a fannoni dabana-daban, don haka suna yin komai ne bisa kwarewa da kulawa.”

..Wani bangaren dattawan majalisar Hakkin mallakar hoto@DRAHMADLAWAN

Wannan zaman lumanar ne ya sa majalisar cimma nasarori da dama, kamar yadda shugaban masu rinjayen ke cewa, ciki har da zartar da kasafin kuɗin kasar na wannan shekarar a farkon shekara, lamarin da ba kasafai yake faruwa ba, da kuma amincewa da kusan dukkan muhimman bukatun da bangaren zartarwa ya tura wa majalisar.

Sai dai kuma wasu masana harkokin siyasa na sukar dangantakar da ke tsakanin bangaren majalisar dattawan da na zartarwa, wadda suka ce ta zarce ta aiki da juna inda suke cewa ta zama tana biyayya ido rufe.

Farfesa Jibrin Ibrahim, jami`i ne na cibiyar raya dimokuradiyya ta CDD kuma yana da irin wannan ra’ayin inda ya bayyana cewa aikin majalisa shi ne su duba duk wasu ayyuka da bangaren zartarwa da kawo domin ganin ko akwai kurakurai su gyara.

Ya ce “wannan aikin nasu shi ne ake gani kamar ba sa yi, shi ya sa yanzu mutane ke kallonsu kamar ‘yan amshin shata.”

..Shugaban majalisar a kan aikinsa Hakkin mallakar hoto@DRAHMADLAWAN

Wasu masana da ‘yan Najeriyar da dama na zargin cewa ‘yan majalisar sun gaza wajen yin aikinsu, saboda a cewarsu hatta kasafin kudin 2020 din ma sun zartar da shi ne ba tare da cikakken nazarinsa ba.

Haka kuma, wasu ‘yan ƙasar suna zargin su da cushen ayyuka. Ko bayan da aka sake mika musu kasafin kuɗin don sake masa fasali bayan bullar cutar korona, wasu na kushe majalisar da rage kason wasu ɓangarori da suka hada da kiwon lafiya da ilimi, amma ba su yi watsi da batun yi wa ginin majalisar dokokin kwaskwarima da wasu biliyoyin naira ba.

Sai kuma sukarsu da ake yi da saurin amincewa da buƙatun shugaban ƙasa da dama ciki har da batun karɓar rancen biliyoyin daloli, wanda watakila sai jikokin da za a haifa gaba ne za su biya bashin, da kuma amincewa da sunayen ministoci da na hukumomi ba tare da tambaya ba.

Sai dai Sanata Yahaya Abdullahi ya ce wani lokaci ana jahiltar yadda suke aikinsu, dangane da maganar rance kuma ya ce za su yi aikinsu na sa ido wajen ganin an kashe kuɗin ta hanyar da ta dace.

”Mu ba mun zo ne a yi wani kalubale da juna ba tsakanin mu da bangaren zartarwa, abin da muka zo shi ne a hada kai da wancan bangaren a yai wa Najeriya aiki. Duk wani kalubale da ba zai kawo maslaha da ci gaban kasa ba to ba shi da amfani gare mu da wadanda suka zabe mu.

”Idan akwai abin da muka ga sun kawo wanda ba zai taimaki ci gaban kasa ba, to ba za ma mu bari a zo ana fallasa a nan ba, tun daga gabatar da shi za mu mayar da shi.” a cewar Sanata Yahaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here