Na Gode Wa ‘Yan Jarida Kan Tabbatar Da Dimokuraɗiyya – Buhari

0
791
Rabo Haladu Daga Kaduna
SHUGABA Muhammadu Buhari ya yaba wa ‘yan jaridar  inda ya siffanta su da cewa “madubin al’umma” ne a fafuti kar tabbatar da dimokuraɗiyya .
Buhari ya bayyana haka ne a jawabin da ya gudanar ga ‘yan ƙasa na ranar dimokuraɗiyya a yau Juma’a, 12 ga watan Yuni.
“Ina son na miƙa godiyata ga ‘yan jarida a fafutikar tabbatar da dimokuraɗiyya tun bayan da muka samu ‘yancin kai,” in ji Buhari.
Ya ci gaba da cewa: “Na sani cewa ba ku fiya samun alaƙa mai kyau ba tsakaninku da gwamnatocin da suka gabata. Sai dai a bayyane take cewa ku ne madubin al’umma na ƙwarai musamman wurin sa ido kan ayyukan gwamnati.”
Game da yaƙin da Najeriya take yi da annobar korona kuwa, Buhari ya ce annobar tana kawo wa dimokuraɗiyyar Najeriya barazana amma yana da ƙarin gwiwar ƙasar za ta kawo ƙarshen cutar.
“Najeriya ta tsira daga rikice-rikice iri-iri a baya. Ina da ƙwarin gwiwa Najeriya za ta tsira daga wannan ma muna masu hangen nesa cikin ikon Allah.”
Buhari ya sauya ranar 29 ga watan Mayu a matsayin Ranar Dimokuraɗiyya a Najeriya zuwa 12 ga watan Yunin kowacce shekara ne tun a shekarar 2018 kuma wannan ne karo na uku da aka yi bikin a sabuwar ranar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here