Ranar Dimokuradiyya: Jawabin Shugaba Buhari Ci Mutuncin Dimokuradiyya Ne – PDP

0
312

Rahoton Z A Sada

JAM’IYYAR adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana jawabin da shugaba Muhammadu Buhari ya yi na ‘Ranar Dimokraɗiyya’ a matsayin “cin mutuncin dimokuraɗiyya”.

PDP ta ce Buhari ba shi da abin da zai nuna da yake tabbatar da cewa shi mai bin ƙa’idojin dimokraɗiyya ne, saboda haka ya gasgata iƙirarin da jam’iyyar ke yi na cewa “ba zai iya mulkar Najeriya ba”.

A martanin da take mayar wa kan bayanin da shugaban ya yi na ranar 12 ga Yuni a matsayin ‘Ranar Dimokraɗiyya’, ta ƙara da cewa Buhari ya gaza kare rayukan ‘yan Najeriya.

“Yan Najeriya sun yi mamaki, yayin da ‘yan bindiga ke kashe mu a Zamfara da Katsina da Kaduna da Borno hatta a jajibirin bayanin nasa, shi kuma yana iƙirarin cewa gwamnati ta samar da tsaro,” in ji sanarwar da PDP ta fitar.

Jam’iyyar ta yi kira ga ‘yan Najeriya da “su farga, kada su bari farfagandar jam’iyya mai mulki ta APC ta rufe musu ido”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here