Taɓarɓarewar Tsaro: Shin Shugaba Buhari Ya Yi Watsi Da Jihar Katsina Ne?

0
970

Rahoton Z A Sada

UMURNIN da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa hukumomin tsaron kasar na kaddamar da sabon yunkuri domin kakkabe ‘yan bindiga da suka addabi jama’a a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin kasar ya zo ne a daidai lokacin da mazauna jihar da dama suka yanke kauna kan kokarin da jami’an tsaro suke yi na shawo kan matsalar.

Jihar ta Katsina, kamar wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya irin su Zamfara da Kaduna, ta dade tana fama da hare-haren ‘yan bindiga wadanda suke kashe mutane, su sace dukiyoyinsu kuma su yi wa mata fyade.

Masu lura da lamuran tsaro sun yi kiyasin cewa wadannan hare-hare sun yi sanadin mutuwar daruruwan mutane da raba dubbai da gidajensu.

Shugaban na Najeriya, a cikin sanarwar da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu, ya aike wa manema labarai ranar Lahadi, ya sha alwashin daukar dukkan matakan da suka kamata wajen murkushe ‘yan bindigar da suka addabi jihar.

A cewar Garba Shehu, matakan sun hada da kai wa ‘yan bindigar hari wuraren da suke maimakon a bari sai sun kai wa jama’a hari kafin a mayar musu da martani.

Sai dai da alama wadannan kalamai na shugaban Najeriya, wadanda ya dade yana yin irin su, ba su shiga kunnen al’umar jihar ta Katsina da ma masu lura da lamuran tsaro ba, wadanda suke ganin gwamnatin Shugaba Buhari, wanda dan asalin jihar ta Katsina ne, babu abin da za ta sauya idan ba a yi wa yaki da ‘yan bindigar abin da Hausawa kan ce kisan-baki-sai-gayya ba.

Ko a karshen makon jiya sai da wasu mazauna yankin karamar hukumar Jibia suka yi zanga-zanga domin nuna matukar bacin ransu game da halin ko-in-kula da suke zargi shugabanninsu suna yi kan batun tsaron jihar.

Hakazalika wasu ‘yan majalisar dokokin jihar ta Katsina sun yanke kauna da matakan da gwamnatin jiha da ta tarayya suke dauka wajen magance matsalar suna masu cewa basu ga alfanun matakan da shugaban kasar yake cewa ana dauka wurin kawo karshen hare-haren ba.

Hasali ma, wasu daga cikin mazauna jihar ta Katsina suna ci gaba da yin hijira zuwa wasu yankunan jihar da ke da saukin matsalar tsaro, da ma wasu jihohin domin tsira a rayukansu. Wasu ma Jamhuriyyar Nijar suke zuwa neman mafaka.

Wani mazaunin yankin Dutsinma ya shaida wa BBC cewa hare-haren da ‘yan bindiga suke kai wa a yankuna sun zama ruwan-dare kuma ikirarin da Shugaba Buhari ya yi cewa zai magance matsalar tsaron jihar ba zai yi wani tasiri ba.

Rundunar 'yan sanda ta ce tana bincikeHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMazauna jihar sun ce jami’an tsaro ba sa kai masu ɗauki sai bayan an kammala kai musu hari

“Ba karamar hukumar Dutsinma kadai ba, Safana, Batsari, Danmusa, da Kurfi da Dutsinma muna cikin halin la’ilaha’ula’i. Kusan kullum wadannan ‘yan bindiga suna kawo hare-hare babu kakkautawa. Kusan koina abin yana watsuwa. Sama da kwana ashirin babu wata rana da ba za ka ji cewa sun je sun yi kisa ko sun yi fyade ko sun kwashe dukiyoyi, ko sun yi duka gaba daya”, a cewar mutumin wanda ba ya so a ambaci sunansa.

An dade ana ruwa kasa tana shanyewa

Ya kara da cewa suna cikin fargaba domin ba su da tabbas kan abin da zai faru da su a kowanne lokaci, inda ya ce abin takaicin ma shi ne jami’an tsaro ba sa kai musu dauki sai an gama kai musu hari.

A cewarsa, gwamnati ba ta da niyyar kare su duk kuwa da cewa tana da karfin yin hakan, inda ya kara da cewa “an dade ana ruwa kasa tana shanyewa. Wannan matsalar ba yau ta faru ba; kusan shekara biyar da aka fara gwamnatin nan muka fara fuskantar wadannan matsalolin. Shugaban kasa ya taba zuwa ya kaddamar da Operation Sharar-Daji. Me ya ayyana? An kashe kudi wajen sayen uniform da makamai amma daga baya babu abin da aka yi.”

Masana harkar tsaro a Najeriya irin su Malam Kabiru Adamu sun bayyana cewa akwai bukatar sauya salon yaki da ‘yan bindigar tun daga matakin al’umma da na karamar hukuma da na jiha, da kuma na tarayya idan ana son magance wannan matsala a Katsina.

A cewarsa” Akwai bukatar a aiwatar da shawarwarin da ke cikin Kundin Tsarin Tabbatar da Tsaro na 2019. Ya kamata a aiwatar da su cikin gaggawa. Abin da ke faruwa [a Katsina] ya fi karfin sojoji kadai; yana bukatar hada gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da ta jiha da kuma kasashen da ke da iyaka da wannan jiha domin a shawo kansa.”

Masu lura a harkokin na tsaro dai suna ganin jihar ta Katsina za ta ci gaba da fuskantar irin wadannan hare-hare idan ba an dauki matakin tabbatar da tsaro a jihohin da ke makwabtaka da ita ba, domin kuwa idan aka koro ‘yan bindigar daga jihohin da ke makwabtaka suna komawa jihar Katsina, kuma idan aka kore su daga Katsina suna komawa makwabtanta.

Kuma da ma wannan matsala ba ta jiha guda ba ce. A wani rahoto da ta fitar, wata kungiya mai bincike kan rikice-rikice a kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce a ilahirin yankin arewa maso yammacin Najeriya an kashe mutane fiye da 8000 cikin shekaru goma da aka kwashe ana fama da matsalar tsaron, wadda kungiyar ta ce a jihar Zamfara aka soma sannan ta bazu zuwa jihohin Katsina, da Sokoto, da Kebbi da ma jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar kasar.

Ta ce kokarin shawo kan lamarin kawo yanzu ya gaza.

Kamar sauran masu lura da lamura, ita ma kungiyar ta International Crisis Group ta ce wajibi ne hukumomi a matakai daban-daban su karfafa matakan sulhu, da kwance damarar mayaka, da kyautata rayuwar jama’a da kuma karfafa ayyukan jami’an tsaro a zahiri muddin ana son kawo karshen tashin hankalin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here