Yau Ake Bikin Zagayowar Ranar Dimokuradiyya A Najeriya

0
373

Rahoton Z A Sada

A Najeriya, ranar 12 ga watan Yunin kowacce shekara ita ce ranar bikin zagayowar Dimokuradiyya ta kasar.

Wannan rana da galibin al’ummar Najeriyar suka fi sani da June 12, rana ce da tarihin kasar ba zai manta da ita ba saboda a ranar ce aka gudanar da zaben Najeriya na 1993, kodayake har kawo yanzu hukumar zaben Najeriyar ba ta sanar da wanda ya lashe zaben ba.

To sai dai kuma dukkan alamu sun nuna cewa dan takarar jam’iyyar SDP, wato Moshood Kashimawo Olawale Abiola, ne ya lashe zaben inda ya kayar da abokin takararsa na jam’iyyar NRC Bashir Othman Tofa.

An dai ki sanar da sakamakon zaben ne saboda soke zaben da gwamnatin mulkin soja a karkashin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi.

Soke zaben dai ya janyo gagarumar tirjiya daga ‘yan jam’iyyar SDP da kuma ‘yan gwagwarmaya da ke da rajin kafa gwamnatin farar hula a wancan lokaci abin da ya kai ga tsare wasunsu da dama ciki har da Abiola.

Wannan rana ta 12 ga watan Yuni, ta kara karfi ne bayan da gwamnatin mulkin dimokuradiyya ta zauna da kafarta a 1999.

An rinka gudanar da bikin wannan rana ne tun daga shekarar 2002, haka kuma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karawa wannan rana karfi a shekarar 2018 bayan da ya sauya ranar dimokuradiyya daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa ranar 12 ga watan Yuni.

Sauya ranar Dimokuradiyya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni bai yi wa wasu ‘yan Najeriyar dadi ba inda har wasu na ganin cewa siyace kawai.

A kowacce rana irin wannan gwamnatin Najeriyar kan bayar da hutu ga ‘yan kasa, sannan ta shirya biki a matakin tarayya, haka suma jihohin kasar musamman na shiyyar arewa maso yammaci kan shirya irin wannan biki da nufin tunawa da ranar da aka yi zaben 12 ga watan Yuni.

A wannan karon dai za ayi bikin zagayowar wannan rana a yanayi na annobar cutar korona, abin da ake ganin bikin wannan shekarar ba zai yi armashi ba saboda yanayin da ake ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here