Matsalar Fyade Na Matukar Tada Min Hankali – Buhari

0
267

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN kasar Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari mai ritaya ya ce yana matukar fusata da annobar fyade da ta kunno kai a Najeriya.

Ya sanar da hakan ne a yayin jawabin ranar damokaradiyya na 2020 a yau Juma’a. Ya ce mulkinsa ya shirya yaki da cin zarafin jinsi ta duk hanyar da ta dace.

Ya ce, “Matan Najeriya har yanzu suna da matukar muhimmanci don haka dole ne a basu matsayi na alfarma a al’amuran kasar nan.

“Ina jinjinawa kwarin guiwarku da jajircewarku tare da gudumawar da kuke badawa wurin habakar kasar nan.

“Ina sanar da dukkan matan da ke fadin kasar nan cewa za mu kawo karshen cin zarafi na jinsi ta hanyar kafa dokoki da kuma wayar da kai.

“Na matukar fusata a kan yadda ake ta yi wa mata fyade da kananan yara. ‘Yan sanda na kan al’amarin da kuma tabbacin za a damko masu laifi tare da ladabtar da su.”

Ana ta zanga-zanga a fadin kasar nan bayan yawaitar fyade ga mata da kananan yara.

Vera Omozuwa budurwa ce mai shekaru 22 wacce aka yi wa fyade tare da kasheta a wata coci da ke Benin City.

Barakat Bello budurwa ce mai shekaru 18 da aka yi wa fyade tare da sassarata a garin Ibadan da ke jihar Oyo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here