An Kaddamar Da Sababbin Shugabannin Jam’iyyar PDP Na Mazabun Karamar Hukumar Lere

  0
  510
  Shugaban jam'iyyar PDP na Karamar Hukumar Lere Alhaji Tasi'u Bala lokacin da yake kaddamar da sabon shugaban PDP

  Isah Ahmed Daga Jos

  AN gudanar taron kaddamar da sababbin shugabannin jam’iyyar PDP na mazabun Karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna guda 11, a ranar asabar din nan, a garin Unguwar Bawa.

  Da yake jawabi a lokacin da yake kaddamar da sababbin shugabannin, shugaban jam’iyyar PDP na Karamar Hukumar Lere, Alhaji Tasi’u Bala ya bayyana cewa an kaddamar da wadannan sababbin shugabanni ne.  Bayan da uwar jam’iyyar ta Jihar Kaduna ta tabbatar da zabensu, kuma ta bayar da umarnin a zo a kaddamar da su.

  Ya ce babu shakka wannan abu da aka yi, an yi abin da magoya bayan jam’iyya na dukkan mazabun Karamar Hukuma suke so.

  Ya  tabbatar da cewa wannan zaben sababbin shugabannin da aka yi, za su kawo dukkan mazabu 11 na Karamar Hukumar a zabe mai zuwa.

  Ya ce dama Karamar Hukuma Lere ta  jam’iyyar PDP ce, kuma ga shi jam’iyyar da ke kan mulki, ta yi abubuwa da dama na na wahalar da jama’a. Don haka babu wata tantanma PDP za ta sake lashe wannan Karamar Hukuma, a zabe mai zuwa.

  Shima a nasa jawabin tsohon mataimakin shugaban Karamar Hukumar Lere Mista Peter Bawa, ya bayyana matukar farin cikinsa kan yadda aka gudanar da zaben sababbin shugabannin  aka kuma  kaddamar da  su lafiya.

  Ya yi  kira ‘ya’yan  jam’iyyar su bai wa wadannan sababbin shugabanni goyan baya da hadin kai, domin jam’iyyar ta sami nasara.

  A nasa jawabin a madadin sababbin shugabannin da aka kaddamar, sabon shugaban jam’iyyar PDP na mazabar Ramin Kura Alhaji Murtala Ramin Kura, ya mika godiyarsu  ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da  shugabannin da suka jagoranci gudanar da wannan zabe, kan yadda suka gudanar da zaben cikin adalci.

  Ya ba da tabbacin cewa za su yi iyakar kokarinsu wajen ganin sun hada kan ‘ya’yan jam’iyyar, a dukkan mazabun karamar Hukuma, don ganin   jam’iyyar ta sami nasara.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here