Mutane Na Gudun Hijira A Wasu Kauyukan Katsina

0
245
Rabo Haladu Daga Kaduna
A’UMMOMIN ƙauyukan yankin Katsina musamman mata da yara na ci gaba da tserewa daga gidajensu saboda ‘ƴan fashin daji da suka addabe su da hare-hare.
Wani mazaunin yankin Hassan Mohammed Daudawa ya shaida wa Manema labarai  cewa mutanen sun koma rayuwa a cikin azuzuwan wasu makarantun Boko na yankin Funtuwa da sauran yankunan da ba a cika kai hare-hare ba.
A ƴan kwanakin nan ƴan bindiga masu fashin daji sun tsawwala hare-hare a yankunan karkara na Katsina inda ko a ranar Juma’a sun shiga garin Mazoji na karamar hukumar Matazu suka kashe Mai Garin Papu Alhaji Dikko Usman Mazoji bayan sun kashe Hakimin Ƴantumaki a makon da ya gabata wanda ya haifar da zanga-zanga a garin.
Maharan sun kuma sun kuma shiga garin ‘Ƴankara da sauran kauyuka a karamar hukumar Faskari da kuma wasu ƙauyuka na Batsari inda suka kashe mutane suka kuma tafi da wasu da dabbobi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here