‘Yan Kasuwa A Kano Na Neman Tallafin Gwamnatin Tarayya 

0
238
Rabo Haladu Daga Kaduna

‘YAN kasuwa a jihar Kano sun bukaci tallafin gwamnatin tarayya domin farfado da hannayen jarinsu na kasuwanci saboda mawuyacin hali da suka shiga sanadiyyar cutar korona, yayin da masana tattalin arziki ke shawartar hukumomin Najeriya su habaka harkokin kasuwar cikin gida.

Kimanin makonni biyu bayan shugaba Buhari ya soke dokar kulle a wasu manyan biranen kasar, gwamnonin Kano da Kaduna na ci gaba da aiki da wannan dokar, a wani mataki na ci gaba da yaki da cutar korona.

Kodayake Gwamnonin sun sassauta dokar domin bai wa jama’a musamman ‘yan kasuwa damar hada hada a wasu ranaku da aka kebe, amma ‘yan kasuwa a Kano na neman kari, kamar yadda shugaban ‘yan kasuwar kantin kwari Alhaji Shariff Sagir ya fada wa manema labarai haka.

Baya ga karancin ranakun hada hada, karayar jari saboda illar korona shi ne babban al’amarin da ke ci wa ‘yan kasuwar tuwo a kwarya don haka suka nemi agajin shugaba Buhari.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da masana tattalin arziki ke jan hankalin hukumomin Najeriya su habbaka lamuran kasuwaninsu na cikin gida a matsayin matakin tada komar tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here