Shin Abin Ban Tsoro Ne Harba Bindiga A Fadar Aso Rock?

0
405

Rahoton Z A Sada

MASU yin sharhi a Najeriya na ci gaba da bayyana abin da ke cikin zukatansu game da hargitsin da ya faru tsakanin jami’an tsaron uwargidan Shugaba Buhari na Najeriya da kuma na ɗan yayarsa ranar Alhamis.

Wasu dai na cewa lamarin wanda rahotanni suka ce har ya kai ga harba bindiga na da ban tsoro, musamman a ce ya faru a fadar shugaban ƙasa.

Farfesa Jibo Ibrahim ya ce ya kasa fahimtar abin da ya yi zafi har aka fitar da bindiga a matsugunnin shugaban ƙasa.

Lamarin dai ya faru ne ranar Alhamis, inda rahotanni ke cewa uwargidan shugaban ƙasar, Aisha Buhari ta yi ƙoƙarin tilasta wa ɗaya daga cikiin mataimakan shugaban na musamman, Sabi’u Yusuf ya je ya killace kansa.

Jibo Ibrahim ya ce: “Ni abu na farko da ya ba ni mamaki shi ne, akwai annoba a cikin ƙasa don haka dole ne akwai sharuɗɗa da za a shirya ga duk jami’in fadar da ya yi tafiya”.

Najeriya dai na fama da annobar korona, wadda zuwa yanzu alƙaluman hukuma ke cewa mutane sama da 16,000 sun kamu, yayin da wasu fiye da 400 kuma suka rasu sanadin cutar.

Gwamnatin ƙasar dai ta haramta tafiye-tafiye tsakanin jihohi, haka kuma ga jami’an da tafiyarsu ta kasance tilas, ƙwararru sun shawarta killace-kai tsawon kwana 14 don kauce wa yaɗa annobar.

Bayanai dai sun ce Sabi’u ya koma fadar shugaban ƙasar ne daga tafiyar da ya yi zuwa Legas, inda ya tuntuɓi Buhari kan lamarin, kuma ya sahale masa ya ci gaba da ayyukansa ba sai lallai ya killace kansa ba.

Aisha BuhariHakkin mallakar hoto@AMUHAMMADUBUHARI
Aisha Buhari – Matar Shugaban Najeriya

Farfesa Jibo ya ce akwai yadda ya kamata babban ofishi kamar na shugaban ƙasa ya yi aiki, sai dai alamun da suke gani na nuna ba haka ofishin shugaban Najeriyan ke aiki ba.

A cewarsa: “Me ma zai kawo iyali ko uwargida ta shiga harkar da ta fi tsaron shugaban ƙasa? Ai likitansa ne ya kamata ya sa doka, don tabbatar tsaron lafiyan shugaban”.

Shi kuwa Babangida Jayawa cewa, ya yi shi Tunde wato Sabi’u ya yi tarin kai ne amma ai bai fi uwargida A’isha son shugaba Buhari ba, domin idan ska gana har cutar ta shigi jikin Bhari, to, dkan iyalan shugaban na cikin rikici..

Kuma ai ba a kansa shi Sabi’u Tunde ba ne kadai aka fara yin hakan ba, don kuwa ko a yayin da aka dawo jana’izar tsohon shugaban ma’aikata, marigayi Abba Khari, an hana Ministoci da ‘Yan majaisu da ma mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Garba Shehu da duk wadanda suka halarci jana’izar shiga fadar shugaban kasa har sai sun killace kansa.

Jayawa ya ce, lallai a nan a yi wa uwargida A’isha uzuri don aiwatar da yadda za ta iyya don ba da kariya ga mijinta Ya ce, idan an duba kullum tana yin abin da za ta iya ne don kare iyalan shugaban kasa kafatansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here