Abiola Ajimobi Ya Zama Shugaban Riƙo Na Jam’iyyar APC

0
801
Rabo Haladu Daga Kaduna
JAM’IYYAR APC mai mulki a Najeriya ta bayyana Sanata Abiola Ajimobi a matsayin wanda zai maye gurbin Adams Oshiomhole, inda zai ci gaba da shugabancin jam’iyyar amma na riƙo
Sakataren yaɗa labaran APC na ƙasa, Lanre Issa-Onilu a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce bayan tuntuɓar sashen harkokin shari’ah na jam’iyyar kuma bisa tanadin sashe na 14 ƙaramin sashe na 2, uku cikin baka na tsarin mulkin APC mataimakin shugabanta na ƙasa shiyyar kudu ne zai ci gaba da jagorantar APC a matsayin riƙo.
Ta ce matakin ya zo ne bayan kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC ya samu labarin da ke nuna cewa kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Oshiomhole.
Rahotanni sun ce a ranar 4 ga watan Maris ne babbar kotun Abuja ta dakatar da shi, ya zuwa lokacin da za ta saurari ƙarar da aka shigar a kansa.
Matakin na zuwa ne sa’o’i bayan fitar Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki daga jam’iyyar APC sakamakon rikicin cikin gida tsakaninsa da Adams Oshiomhole.
Tinubu ya ce ana kassara APC saboda zaben 2023
Batun sake tsayawa takarar Obaseki na daga cikin abubuwan da suka janyo ɓaraka tsakaninsa da tsohon ubangidansa na siyasa Oshiomhole.
Wannan ɓaraka ce kuma ta haddasa darewar APC zuwa gida biyu a jihar Edo, inda Oshiomhole ya yi gwamna kafin Obaseki ya gaje shi.
Wasu kafofin yaɗa labarai  sun ambato Obaseki na neman Oshiomhole ya matsa gefe daga harkar fitar da mutanen da za su yi zaɓen fid da gwani a APC, sai dai jam’iyyar ta ƙi amincewa da buƙatarsa.
Obaseki ya bayyana wa manema labarai bayan ganawarsa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya a Abuja cewa zai koma wata jam’iyyar domin neman takara a wa’adin mulki na biyu.
A makon da ya wuce ne APC ta ce Obaseki ba zai iya shiga zaben fitar da gwani ba a jam’iyyar saboda a cewarta akwai bayanai masu saɓani da juna a takardun karatunsa.
Tun lokacin da kwamitin tantance masu neman takarar gwamna na jam`iyyar APC ya tabbatar da cire shi daga cikin wadanda ya tantance, Gwamna Godwin Obaseki ya fada mawuyacin hali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here