An Gudanar Da Zanga-Zanga Bisa Zargin Yawaitar Fyade A Benuwai

0
330

Daga Usman Nasidi.

GAMAYYAR wasu mambobin kungiyoyi sun mamaye yankin Otukpo a jihar Benuwai domin gudanar da zanga – zangar nuna jin rashin jin dadinsu a kan samun yawaitar matsalar aikata fyade ga ‘ya’ya mata a yankin da fadin jihar.

An shirya zanga – zangar ne a karkashin gamayyar kungiyoyin da ke yaki da aikata fyade a jihar Benuwai (BeCare).

Jagororin zanga – zangar sun bayyana damuwarsu a kan yadda aka samu matsalar aikata fyade har 8 a cikin mako guda a iya yankin Otukpo kadai.

Da yake magana da manema labarai, jagoran masu zanga – zangar, Prince Yemi Itodo, ya ce sun shirya zanga-zangar ta lumana ne domin wayar da kai a kan illolin da ke tattare da aikata fyade da kuma neman a kawo karshen matsalar.

A kalmomin Itodo: “mun shirya wannan zanga – zanga domin nunawa masu jin dadin aikata fyade cewa abinda suke yi ba daidai ba ne, lokaci ya yi da ya kamata su sauya, su nemi sabuwar rayuwa.

“A cikin mako daya kawai, an yi wa yara mata 8 fyade a sassan kananan hukumomin jihar Benuwai, amma mutum 3 ne kacal a hannun rundunar ‘yan sanda .”

Masu zanga – zangar sun bi ta cikin garin Otukpo zuwa ofishin rundunar ‘yan sanda, sannan suka bulle ta gaban sakatariyar karamar hukuma zuwa ta gaban fadar babban sarkin masarautar Otukpo/Ohimini.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here