An Kori Janar A Rundunar Sojin Najeriya ‘Babu Girma, Babu Arziki’

0
337

Daga Usman Nasidi.

WATA babbar kotun sojoji da ke zamanta a Abuja ta zartar da hukunci a kan tsohon kwamandan rundar sojojin jihar Sokoto, Manjo Janar Hakeem Oladapo Otiki, bayan an gurfanar da shi a gabanta bisa tuhumarsa da laifin satar kudin rundunar soji.

Kotun ta sanar da cewa ta samu hannun Janar Otiki a cikin dukkan tuhuma biyar da aka gurfanar da shi a gabanta dasu.

A saboda haka, kotun ta sanar da cewa ta zartar da hukuncin korar Janar Otiki daga aiki ‘ babu girma, babu arziki’.

A cewar kotun, wacce ke karkashin Laftanal Janar Lamidi Adeosun, ta samu Otiki da laifin rashin da’a da biyayya ga dokokin aikin rundunar soji tare da samunsa da laifin sata da karkatar da kadarar gwamnati da sauran wasu laifukan.

Duk da an kore shi daga aiki, kotun ta sanar da cewa an rage masa matsayi zuwa birgediya janar.

Hukuncin zai fara aiki bayan kwamitin koli na rundunar soji ya rattaba hannu a kansa.

Kotun ta bukaci kwamitin bincike na musamman da aka kafa ya mayar da miliyan N135.8 da aka samu a wurin janar Otiki zuwa asusun rundunar soji.

Kazalika, rundunar soji ta bukaci a mallaka mata wata miliyan N150 da aka gano janar Otiki ya mallaka, kuma ya kasa bayyana tushensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here