Fyade Wata Babbar Matsala Ce A Najeriya-Ustaz Imam Gana

0
694
Ustaz Abubakar Imam Bala Gana

Isah Ahmed Daga  Jos 

DARAKTAN ilmi na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah ta kasa, reshen Jihar Filato Ustaz Abubakar Imam Bala Gana ya bayyana cewa halin da aka shiga, na yawaitar aikata fyade a Najeriya wata babbar matsala ce. Ustaz Abubakar Imam Gana ya bayana haka ne, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.

Ya ce wannan mummunar dabi’a ta fyade tana da illoli da dama, da suka hada da  jawo nakasar rayuwa da yada cututtuka  da dai sauransu.

Ya ce babban abin da yake kawo wannan mummunar dabi’a, shi ne rashin tarbiyya domin idan mutum yana da tarbiyya, ba zai je ya kama yar wani da karfi, ya yi lalata da ita ba.

Ya ce mu ‘yan adam a addinin musulunci muna da tsari, na idan aure ne mutum zai yi,  sai anje an tambaya an sami izini. To ka ga duk wanda ya yi wa wata fyade, bai bi tarbiyyar addinin musulunci ba.

 ‘’Hanyar magance wannan matsala ita ce  a sassauta sadakin aure. Idan mutum yazo zai nemi diyarka ka duba idan yana da sana’a, kuma an yarda da addininsa, sai a ba shi auren. Bai kamata mutane su rika raina sana’ar wadanda suka zo neman ‘ya’yansu ba. domin irin wannan yana sa matasa su shiga cikin wannan mummunar dabi’a ta fyade a kasar nan’’.

Ustaz Abubakar Gana ya yi godiya ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi, kan yadda suka sassauta dokokin kare yaduwar annobar cutar korona da suka sanya. Domin wasu kasashen duniya ba su so a yi haka ba.

Ya ce babu shakka mun ji dadi  da wannan mataki da aka dauka, domin yanzu mutane zasu sami damar suje su yi ibada a masallatai, kuma su yi addu’ar Allah ya yaye mana wannan annoba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here